Hajj Mabrur: Hukumar NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazai Zuwa Gida Najeriya
- Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta kawo ƙarshen aikin jigilar Alhazan Najeriya daga ƙasa mai tsarki zuwa guda
- Jirgin ƙarshe wanda yake ɗauke da Alhazan jihar Kwara zai baro ƙasa mai tsarki a ranar Talata, 16 ga watan Yulin 2024
- Shugaban hukumar, Jalal Arabi, ya bayyana cewa tuni shirye-shirye suka kankama kan aikin Hajji na shekarar 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) za ta kammala jigilar maniyyatan Najeriya daga Saudiyya a yau Talata
Mai magana da yawun hukumar, Fatima Usara, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja.
An kammala jigilar Alhazan Najeriya
Ta ce rukunin ƙarshe na Alhazan 2024 na shirin tashi daga filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz da ke Jeddah zuwa Najeriya, cewar rahoton jaridar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce adadin maniyyata 312 daga jihar Kwara za a yi jigilarsu zuwa Ilorin a jirgin Air Peace, wanda zai kawo ƙarshen kammala jigilar Alhazan na bana.
"A zangon farko na aikin Hajji, NAHCON ta gudanar da jigilar maniyyata a jirage 121, wanda a yanzu aka rage zuwa jirage 119 a wajen dawowa."
"An samu raguwar jiragen ne saboda amfani da dukkanin kujerun da ake da su yayin jigilar dawowa."
"Jigilar dawo da Alhazan ta kammala kwanaki uku kafin zuwan lokacin da aka tsara wanda tun da farko aka shirya kammalawa a ranar, 19 ga watan Yulin 2024."
- Fatima Usara
NAHCON ta fara shirin Hajjin 2025
A wajen bikin kammala jigilar Alhazan a filin jirgin sama na Jeddah, shugaban hukumar NAHCON, Jalal Arabi ya nuna godiyarsa ga Allah bisa kammala jigilar Alhazan cikin nasara, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Ya yi alƙawarin cewa hukumar za ta samu gagarumar nasara a shekara mai zuwa duba da darussan da ta koya a bana.
Jalal Arabi ya kuma bayar da tabbacin cewa tuni aka fara shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025.
Alhazan Najeriya mutum 65,000 ne suka sauke farali a ƙasa mai tsarki a bana, inda sama da mutum 50,000 suka bi ta hannun NAHCON yayin da sama da mutum 13,000 suka bi jiragen ƴan kasuwa.
Mahajjaci ya mayar da kuɗin tsintuwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mahajjaci ɗan Najeriya ya yi abin kirki na mayar da makudan kudin da ya tsinta a ƙasa mai tsarki yayin aikin Hajji.
Hukumar NAHCON ta tabbatar da cewa mahajjacin ya samu kudin tsintuwa da suka kai €1,750 waɗanda za su kai N2.8m a garin Makka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng