Gwamna Ya Aike da Saƙo Bayan Ɗan Majalisar Tarayya Daga Kaduna Ya Rasu

Gwamna Ya Aike da Saƙo Bayan Ɗan Majalisar Tarayya Daga Kaduna Ya Rasu

  • Malam Uba Sani ya aike da saƙon ta'aziyya ga iyalan Hon Ekene Abubakar Adams, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Chikun/Kajuru
  • Gwamna Uba Sani ya bayyana marigayin a matsayin ɗan siyasa mara tsoro wanda ya sadaukar da kansa wajen yi wa al'umma hidima
  • Ekene Adams dai ya riga mu gidan gaskiya da sanyin safiyar ranar Talata, 16 ga watan Yuli bayan fama da rashin lafiya yana da shekaru 39 a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, ya yi ta'aziyyar rasuwar dan majalisar wakilai, Hon Ekene Abubakar Adams.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Chikun/Kajuru a jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar Labour Party (LP), ya rasu ne da safiyar ranar Talata yana da shekaru 39.

Kara karanta wannan

Mutuwar dan majalisa ta girgiza Tinubu, ya mika sakon ta'aziyya

Malam Uba Sani.
Gwamna Uba Sani ya yi ta'aziyyar raauwar Hon Ekene Abubakar Adams Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Twitter

Har zuwa rasuwarsa, marigayin shi ne shugaban kwamitin wasanni na majalisar dokokin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Uba Sani ya miƙa sakon ta'aziyya

Da yake ta'aziyyar rasuwar ɗan majalisar a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X, Gwamna Uba Sani ya ce labarin ya girgiza shi.

Uba Sani ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi Ekene Abubakar Adams da ɗaukacin al'ummar mazaɓar Chikun/Kajuru.

Gwamnan ya kuma yabawa marigayi dan majalisar inda ya ayyana shi a matsayin "ɗan siyasa mara tsoro kuma jagora."

"Honorabul Ekene Adams ya tafi a daidai lokacin da muke bukatar gudummuwarsa, amma duk da haka ya tafi ya bar mana gadon aiki tukuru da hidima ga al'umma."
"A madadin gwamnati da jama'ar jihar Kaduna, ina mika sakon ta'aziyya ga Iyalan Ekene da daukacin al'ummar mazaɓar Chikun/Kajuru da shugaban majalisar wakilai da mambobi.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta karrama ɗan majalisar da Allah ya yiwa rasuwa yau

"Muna addu'ar samun salama ga Hon. Ekene, Ubangiji Allah ya bai wa iyalansa kwarin guiwar jure wannan rashi mara misaltuwa.

- Uba Sani.

Majalisar dattawa ta karrama Ekene

A wani rahoton kuma Majalisar dattawa ta Najeriya ta dakatar da harkokinta na ranar Talata sakamakon rasuwar Hon Ekene Abubakar Adams daga jihar Kaduna

Ekene Aɗams mai wakiltar Chikun da Kajuru a majalisar wakilai ta ƙasa ya rasu ne da sanyin safiyar Talata, 16 ga watan Yuli 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262