Mutuwar Dan Majalisa Ta Girgiza Tinubu, Ya Mika Sakon Ta'aziyya

Mutuwar Dan Majalisa Ta Girgiza Tinubu, Ya Mika Sakon Ta'aziyya

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar Honorabul Ekene Adams wanda ke wakiltar Chikun/Kajuru a majalisar wakilai
  • Shugaba Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga majalisar tarayya da gwamnatin jihar Kaduna kan rasuwar ɗan majalisar
  • Honarabul Ekene Adams ya rasu ne a ranar, 16 ga watan Yulin 2024 mako guda bayan wani ɗan majalisar wakilai ya rasu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyyarsa kan rasuwar ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓun Chikun/Kajuru na jihar Kaduna, Honorabul Ekene Adams.

Shugaban ƙasan ya jajantawa majalisar dokokin tarayya da gwamnatin jihar Kaduna bisa wannan rashin na ɗan majalisar da aka yi.

Kara karanta wannan

Ana batun zanga zanga, Shugaba Tinubu ya ba jami'an tsaro wani umarni

Tinubu ya yi ta'aziyyar dan majalisan da ya rasu
Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar dan majalisar wakilai daga Kaduna Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar dan majalisa

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Cif Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga iyalai da abokan marigayin, inda ya buƙace su da fawwalawa Allah komai, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

"Shugaba Tinubu na addu'ar Allah ya sanya ran ɗan majalisar da ya rasu ya huta ya kuma ba iyalansa juriya."

- Ajuri Ngelale

Ƴan majalisa sun riga mu gidan gaskiya

Ɗan majalisar na jam'iyyar LP yana da shekaru 39 a lokacin mutuwarsa.

Ekene Adams wanda wannan ne karonsa na farko na zuwa majalisar, ya jagoranci kwamitin majalisar wakilai kan harkokin wasanni.

Ɗan majalisar na LP shi ne na uku a cikin ƴan majalisar da ya mutu a wannan shekara. Mutuwar tasa ta zo ne kimanin mako guda bayan wani ɗan majalisar wakilai Olaide Akinremi ya rasu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya aike da saƙo bayan ɗan majalisar tarayya daga Kaduna ya rasu

Akinremi wanda aka fi sani da Jagaban ya wakilci mazabar Ibadan ta Arewa a karkashin inuwar APC.

Dan majalisar ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekara 51 a duniya.

Rasuwa ta sa majalisar dattawa dakatar da aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, ta dakatar da duk wasu ayyukan majalisa na ranar domin karrama marigayi Hon. Ekene Abubakar Adams.

Ekene Abubakar Adams mamba mai wakiltar mazaɓar Chikun da Kajuru a majalisar wakilan tarayya ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Talata, 16 ga watan Yulin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng