Majalisar Dattawa Ta Karrama Ɗan Majalisar da Allah Ya Yiwa Rasuwa Yau
- Majalisar dattawa ta Najeriya ta dakatar da harkokinta na yau Talata sakamakon rasuwar Hon Ekene Abubakar Adams daga jihar Kaduna
- Ekene Aɗams, mamba mai wakiltar Chikun da Kajuru a majalisar wakilai ta ƙasa ya rasu ne da sanyin safiyar Talata, 16 ga watan Yuli
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya jagoranci shirun minti ɗaya domin karrama marigayin kuma daga bisani ya ɗage zama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar dattawa a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, ta dakatar da duk wasu ayyukan majalisa na ranar domin karrama marigayi Hon. Ekene Abubakar Adams.
Ekene Abubakar Adams mamba mai wakiltar mazaɓar Chikun da Kajuru a majalisar wakilan tarayya ya rasu ne da sanyin safiyar yau Talata.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, marigayin ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da rashin lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin rasuwarsa, Honorabul Ekene Adams ya kasance shugaban kwamitin kula da harkokin wasanni na majalisar dokoki ta ƙasa.
Tuni dai majalisar ta tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.
"Majalisar wakilai na jimamin sanar da rasuwar ɗaya daga cikin mambobinta Ekene Abubakar Adams (LP, Kaduna) wanda ya rasu da safiyar Talata yana da shekaru 39," in ji sanarwar.
Majalisar dattawa ta girmama marigayin
Shugaban majallisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da mutuwar Hon Ekene Abubakar Adams a zaman sanatoci na yau Talata a Abuja.
Bayan haka ne majalisar ta yi shiru na tsawon minti ɗaya domin girmama marigayi ɗan majalisar.
Daga nan kuma Sanata Akpabio ya sanar da ɗage zaman majalisar dattawa na yau domin jimami da karrama Marigayi Ekene.
Majalisa ta koka kan haƙar ma'adanai
A wani rahoton kuma kun ji cewa Majalisar wakilai ta ƙasa ta bayyana takaici kan yadda kasar nan ke tafka asara kan hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.
Shugaban kwamitin ma'adanai, Jonathan Gbefwi ya ce ana asarar akalla $9bn duk shekara, wanda hakan ba karamar asara ba ce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng