Babbar Kotu Ta Bada Sabon Umarni ga Aminu Ado Bayero da Sauran Sarakunan da Aka Tsige

Babbar Kotu Ta Bada Sabon Umarni ga Aminu Ado Bayero da Sauran Sarakunan da Aka Tsige

  • Babbar kotun jihar Kano ta tura umarni ga sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu da Gwamna Abba Kabir ya tsige
  • Mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta umarci Aminu da sauran sarakunan su miƙa dukkan kayan gidan sarauta ga gwamnatin jihar Kano
  • Haka nan kuma ta haramtawa sarakunan guda biyar ci gaba da bayyana kansu a matsayin sarakunan Bichi, Rano, Ƙaraye da Gaya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Babbar kotun jihar Kano ta bayar da sabon umarni ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu da aka tube wa rawanin sarauta.

Kotun ta umarci sarakunan guda biyar su tattara dukkan kayan sarauta da ke hannunsu, su miƙawa gwamnatin jihar Kano ko kuma Sarki na 16, Muhammadu Sanusi.

Kara karanta wannan

Karshen tika tika: Kotu ta yanke hukunci kan dambarwar masarautar Kano

Sanusi, Abba da Aminu Bayero.
Kotu ta umarci Aminu Ado ya mayar da kayan sarauta ga Muhammadu Sanusi II Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf, Aminu Ado Bayero
Asali: UGC

Kamar yadda The Nation ta ruwato, kotun ta umarci sarakunan su miƙa kayan sarautar nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta hana Aminu amsa sunan Sarki

Idan ba ku manta ba mun kawo muku rahoton cewa kotun ta hana Aminu Ado da sauran sarakuna huɗu amsa sunan sarakuna a jihar Kano.

Mai shari'a Amina Aliyu ce ta yanke wannan hukunci ranar Litinin, 15 ga watan Yuli a karar da gwamnatin jihar Kano ta shigar gabanta.

Ta kuma haramtawa duka waɗanda sarakunan biyar suka naɗa a wata sarauta daga nuna kansu a matsayin sarakuna, rahoton Channels tv.

Tun farko gwamnatin Kano ta umurci Aminu Ado da sarakunan da ta tuɓe su bar masarautunsu cikin sa'o'i 48 daga lokacin da aka tsige su.

Bisa haka ne mai shari'a Amina ta umarci sarakunan su mika dukkan kadarorin gidan sarauta da ke hannunsu ga gwamnatin Kano ko sarki na 16 Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

"Muhimman cigaba 3 da za a gani bayan samun 'yanci" Inji Tsohon shugaban karamar hukuma

Kwankwaso ya faɗi dalilin tuɓe Sarkin Kano

A wani rahoton kuma kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana musabbabin tuge sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Kwankwaso ya ce Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya dauki matakin ne saboda cika alkawuran da ya daukar al'umma a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262