Bola Tinubu Ya Shiga Taron FEC a Aso Villa, An Yi Shirun Minti 1 Saboda Mutuwar Jigo
- Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron majalisar zartaswa ta tarayya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin, 15 ga watan Yuli
- Kafin fara taron majalisar ta yi shiru na tsawon minti ɗaya domin girmama marigayi Ahmed Muhammed Gusau wanda ya rasu a watan Mayu
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, Nuhu Ribadu da wasu manyan ƙusoshin gwamnatin tarayya sun halarci taron a Aso Villa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron majalisar zartaswa (FEC) yanzu haka a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Wannan taro dai na zuwa ne biyo bayan matakin da majalisar ta ɗauka a makon jiya na ɗage tattaunawa kan wasu muhimman ayyuka da ke ƙarƙashin ma'aikatar ayyuka.
Bola Tinubu ya jagoranci zaman FEC
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ce ayyukan da matakin ya shafa sun ƙunshi wadanda aka gada daga gwamnatocin baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda The Nation ta ruwaito, gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakin ne domin tabbatar da an sa natsuwa da kwarewa wajen aiwatar da ayyukan.
Majalisar FEC ta yi shirun minti 1
Gabanin fara taron FEC na yau Litinin, 15 ga watan Yuli, 2024, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya sanar da rasuwar Alhaji Ahmed Muhammed Gusau.
Marigayin ya kasance tsohon 'dan majalisar zartaswa ta tarayya kuma tsohon mataimakin gwamna a tsohuwar jihar Sakkwato.
Bisa haka ne Akume ya buƙaci a yi shirun minti ɗaya domin girmama marigayin wanda Allah ya yiwa rasuwa a watan Mayun 2024, Daily Trust ta ruwaito.
Shettima da sauran waɗanda suka halarci FEC
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da mai bai shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu.
Sauran sun haɗa da shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folashade Yemi Esan, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila da wasu ministoci.
Tinubu ya sauya shugaban HYPREP
A wani rahoton kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana korar Olufemi Adekanmbi a matsayin shugaban gudanarwa na shirin HYPREP.
Wannan na zuwa ne bayan kwanaki biyu da nada shi shugaban hukumar, ya maye gurbinsa da tsohon shugaban da aka tube.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng