Ana Tsaka da Wahalar Abinci: An Samu Karin Hauhawar Farashin Kayayyaki a Najeriya
- Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa an samu karuwar farashin kayayyaki zuwa 34.19% a watan Yunin 2024
- NBS ta bayyana hakan ne a wani rahoton da ta fitar wanda ta nuna cewa lamarin ya cigaba da kazanta ana tsaka da matsalar abinci
- An samu karin farashin kayayyakin da kashi 0.24 idan aka kwatanta kimar farashin a watannin Afrilu da Mayun 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Farashin kayayyaki a Najeriya ya yi tashin gwauron zabi inda ya kai kashi 34.19 a watan Yunin 2024, daga kashi 33.95% a watan Mayu.
Wannan bayanan an samo su ne daga hukuma kididdiga ta kasa (NBS) a rahoton farashin kayayyaki da ta fitar na watan Yuni a ranar Litinin.
Ma'aunin CPI da hukumar NBS ta yi amfani da shi ya auna ƙimar canjin da aka samu a farashin kayayyaki da biyan kudin gudanar da ayyuka, inji rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton NBS ya nuna tashin farashin kaya
Kamar yadda hukumar ta ce, hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 40.87% a watan Yuni yayin da farashin kayan abinci da kayan sha suka cigaba da tashi.
A cewar rahoton Premium Times, hukumar ta ce an samu karin kashi 0.24% na hauhawar farashin kayayyakin a watan Yuni idan aka kwatanta da kimar na watan Mayu.
"Idan aka duba farashin shekara-shekara, an samu karuwar hauhawar farashin kayayyakin da kashi 11.40 idan aka kwatanta da na Yunin 2023 wanda ya kai kashi 22.79."
"Bugu da kari, idan aka duba farashin wata-wata, farashin kayayyakin a watan Yunin 2024 ya zarce da kashi 2.31 idan aka kwatanta da farashin kaya a watan Mayun 2024."
- Rahoton NBS.
IMF tayi hasashen saukar farashi
A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa, asusun bada lamuni na duniya, IMF, ya bayyana cewa akwai yiwuwar saukar farashin kayayyaki a Najeriya cikin 2025.
IMF bai tsaya a nan ba, ya kara da hasashen cewa za a samu hauhawar tattalin arziki tare da habakarsa a shekarar 2025 duba da yadda ake noma da kiwo a kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng