"Gwamnatin Tinubu ta Zuba Ido Ana Kashemu," Dattawan Katsina Sun Dauki Zafi

"Gwamnatin Tinubu ta Zuba Ido Ana Kashemu," Dattawan Katsina Sun Dauki Zafi

  • Wata kungiyar dattawan jihar Katsina ta bayyana takaicin yadda gwamnatin Bola Tinubu ke wasarere da rayukan 'yan kasa
  • Kungiyar, ta bakin sakatarenta Malam Aliyu Mohammed ta zargi gwamnati da kokarin kawo auren jinsi da dangoginsa ga 'yan Najeriya
  • Haka kuma dattawan na zargin shugaban kasa da sauran kusoshin gwamnati da kin nuna damuwa ga yadda ake kashe jama'ar Katsina

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Dattawa a jihar Katsina sun caccaki yadda gwamnatin tarayya ta zuba idanu kan 'yan kasar nan ana shan bakar wahala.

Kungiyar dattawan Katsina ta KSEF ta kuma bayyana damuwa a kan yadda gwamnati ta yi rikon sakainar kashi da batun tsaro da zargin kokarin kakabawa kasa kudurin halasta auren jinsi da dangoginsa.

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi: "Yanzu jama'a za su sharbi romon dimokuradiyya," APC

Asiwaju
Dattawan Katsina sun caccaki tsarin mulkin Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa sakataren kungiyar, Malam Aliyu Mohammed ya zanta da manema labarai a Katsina inda ya ce mutanen jihar na cikin tsaka mai wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gwamnati ta ki taimakon Katsina," KSEF

Dattawan jihar Katsina sun caccaki yadda gwamnatin Bola Tinubu ta nade hannayenta ta na kallon jihar na fafutuka cikin talauci da rashin tsaro, Sahara Reporters ta wallafa.

Sakataren kungiyar dattawan, Malam Aliyu Mohammed ya ce duk da korafi da su ka mika ga shugaban kasa, har yanzu an ki a yi wani hobbasa domin hana kashe su.

Malam Aliyu ya ce 'yan ta'adda na ta kashe su babu dare babu rana, ana kona dukiyoyinsu da hana su noma a gonaki.

"Gwamnatin Katsina na kokari," in ji KSEF

Kungiyar dattawan jihar Katsina ta bayyana takaicin yadda gwamnatin tarayya ta gaza taimakon kokarin da jihar ke yi na dakile ayyukan rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Auren jinsi: Malaman Katolika sun ba gwamnatin Tinubu zabi 2 kan yarjejeniyar Samoa

Kungiyar ta ce yanzu idan mutum ya fita daga gida, ba ya sa ran lallai zai dawo saboda ta'azzarar rashin tsaro a jihar.

Sakataren kungiyar, Aliyu Mohammaed ya kara da bayyana rashin jin dadi na yadda aka kashe daruruwan jama'a a, amma babu wanda ya iya yi masu ta'aziyya daga cikin kusoshin gwamnati.

Tsaro: Gwamnan Katsina ya nemi taimako

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta nemi daukin jama'a domin dakile matsalar tsaro da ke kara kamari.

Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda ya nemi jama'a da su dage da addu'a domin neman taimakon Allah (SWT) wajen kawo karshen matsalar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.