Sukar Shugaba Tinubu Ta Jawo Sanatan Arewa na Fuskantar Barazana a Zaben 2027

Sukar Shugaba Tinubu Ta Jawo Sanatan Arewa na Fuskantar Barazana a Zaben 2027

  • Gamayyar ƙungiyar dattawan Arewa maso Gabas (CNEF) ta ja kunnen Sanata Ali Ndume kan sukar shugaban ƙasa Bola Tinubu
  • Ƙungiyar ta buƙaci sanatan da ya fito ya bayyana yadda ya gudanar da wakilcinsa a majalisa ko ya rasa kujerarsa a zaɓen 2027
  • Hakan na zuwa ne dai bayan sanatan ya caccaki gwamnatin Tinubu kan halin yunwa da ake ciki a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gamayyar ƙungiyar dattawan Arewa maso Gabas (CNEF) ta yi zargin cewa shekara 20 da Sanata Ali Ndume ya yi a majalisar tarayya bai amfani jihar Borno ba.

Ƙungiyar ta buƙace shi da ya daina sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ko ta sanya ya rasa kujerarsa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta caccaki Sanata Ndume kan sukar Shugaba Tinubu

An gargadi Sanata Ali Ndume
Kungiyar CNEF ta gargadi Ali Ndume kan sukar Shugaba Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sen. Mohammed Ali Ndume
Asali: Facebook

Dattawan Arewa sun ja kunnen Ali Ndume

Dattawan sun buƙaci Ndume da ya taimaki ɗan uwansa daga Borno, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, maimakon sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattawan na yankin Arewa maso Gabas sun fusata ne kan kalaman da sanatan ya yi a kwanan nan kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda suka bayyana a matsayin bai kamata ba, rahoton Politics Nigeria ya tabbatar.

Martanin ƙungiyar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ke ɗauke da sa hannun jagoranta, Alhaji Ali Ibrahim Sheriff.

A cewar dattawan, sanatan wanda ke wakiltar Borno ta Kudu, bai yi amfani da shekara 20 da ya yi a majalisa ba wajen sauya halin da ake ciki.

CNEF ta caccaki Sanata Ndume

"A matsayinmu na dattawan yankin Arewa maso Gabas, muna mamakin dalilin da ya sa a lokacin Shugaba Buhari ya zaɓi ya yi shiru duk da matsalolin rashin tsaro, yunwa, wawure dukiyar jama’a da rashin shugabanci na gari."

Kara karanta wannan

Daga karshe Gwamna Zulum ya fadi dalilin kai harin kunar bakin wake a Borno

"Idan shugabanci abu ne mai sauƙi, mu na tambayarsa da babbar murya a tsawon waɗannan shekaru, ƴan gudun hijira nawa ya horar, ya ba su ilmi da sana'o'i da kuɗaɗen da aka ba shi?"
"Ya kamata Ndume ya fito ya bayyana yadda ya gudanar da wakilcinsa ko mu sanya a ƙi zaɓensa a 2027."

- Alhaji Ali Ibrahim Sheriff

APC ta caccaki Ndume kan sukar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta caccaki Sanata Ali Ndume bisa kalaman da ya yi kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

APC ta bayyana cewa kalaman Ndume na cewa ba a ganin shugaban ƙasan kuma bai san halin da ake ciki a ƙasar nan ba, ba su dace ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng