Dangote Ya Fadi Dalilin Kasa Mallakar Gidan Kansa a Landan Ko Amurka

Dangote Ya Fadi Dalilin Kasa Mallakar Gidan Kansa a Landan Ko Amurka

  • Hamshaƙin attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa a gidan haya yake zama idan ya je Abuja
  • Dangote ya bayyana cewa bai mallaki gida ba a birnin Landan ko a ƙasae Amurka saboda baya son abin da zai ɗauke masa hankali
  • Hamshaƙin attajirin ya bayyana cewa son kafa masana'antu a Najeriya ne ya sanya ba ya da gidaje a ƙasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ba shi da gida a birnin Landan ko a ƙasar Amurka.

Dangote ya kuma bayyana cewa gidan da yake zaune a duk lokacin da yaje babban birnin tarayya Abuja, ba nasa ba ne.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan an hallaka jami'in hukumar kwastam a Jigawa

Dangote ba ya da gida a Landan
Dangote ya ce a gidan haya yake zaune a Abuja Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Attajirin mai kuɗin ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a matatar man Dangote da ke Ibeju-Lekki a jihar Legas a ranar Lahadi, 14 ga watan Yulin 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Dangote bai da gida a Landan ko Amurka?

Dangote ya ce sha’awar da yake da ita na son ganin Najeriya ta samu ci gaban masana’antu shi ne kaɗai dalilin da ya sa ba ya da gidaje a ƙasashen waje, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ya bayyana cewa ya taɓa yin gida a birnin Landan, amma ya cefanar da shi a shekarar 1996.

"Dalilin da ya sa ba ni da gida a Landan ko Amurka shi ne kawai domin ina son na mayar da hankali kan kafa masana'antu a Najeriya."
"Na yi tunanin cewa idan ina da waɗannan gidajen, akwai dalilin da zai sanya na riƙa ziyartar wuraren wanda hakan zai riƙa ɗauke min hankalina."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta caccaki Sanata Ndume kan sukar Shugaba Tinubu

"Ina matuƙar sha'awa sosai kan mafarkin Najeriya kuma ban da gidana na Legas, ina da wani a jihar Kano da kuma na haya a Abuja."

- Aliko Dangote

Karanta wasu labaran kan Dangote

Dangote zai yi ayyuka a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote zai gudanar da ayyuka a jami'ar jihar Kano da ke Wudil wacce aka sanyawa sunansa.

Alhaji Aliko Dangote ya kuma sharewa jami'ar hawaye wajen biya mata bashin kuɗaɗen wutar lantarki har Naira miliyan 100 da aka biyo ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng