Jam'iyyar APC Ta Caccaki Sanata Ndume Kan Sukar Shugaba Tinubu
- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a Najeriya ta nuna rashin jin daɗin ta bisa kalaman da Sanata Ali Ndume ya yi kan shugaban ƙasa Bola Tinubu
- A cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar na ƙasa, Felix Morka, ya fitar ya bayyana cewa kalaman na Ndume sun yi kama da na wanda yake son shugaban ƙasan ya gaza
- Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana mayar da hankalinsa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na shugaban ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta caccaki Sanata Ali Ndume bisa kalaman da ya yi kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
APC ta bayyana cewa kalaman Ndume na cewa ba a ganin shugaban ƙasan kuma bai san halin da ake ciki a ƙasar nan ba, ba su dace ba.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya fitar, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane martani APC ta yiwa Sanata Ali Ndume?
A cikin sanarwar ya buƙaci Ndume da ya daina ƙoƙarin neman sunan da yake yi a kafafen yaɗa labarai, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
"Ba abin mamaki ba ne idan Sanata Ndume ya ji takaicin rashin samun damar ganawa da shugaban ƙasa. Amma hakan bai zama hujjar da zai sanya ya ce an keɓe shugaban ƙasan ba kuma bai san halin da ake ciki ba a ƙasa."
"Kalaman Ndume sun yi kama da na mai son ganin shugaban ƙasa ya gaza."
"Shugaban ƙasa yana can yana aikin da ƴan Najeriya suka zaɓe shi ya yi. Shi ne shugaban gwamnati wanda yake da ikon duba ƙalubalen kowane ɓangare."
"Yana da kyau shugaban ƙasa ya yi amfani da lokacin da yake da shi yadda ya dace domin muhimman al'amuran ƙasa."
- Felix Morka
Sanatan APC ya caccaki Ali Ndume
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Sunday Karimi mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa, ya gargadi Sanata Ndume kan sukar shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Sanatan na Kogi ya nuna cewa Ali Ndume ya yi shiru lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari saboda ya fito daga Arewacin Najeriya
Asali: Legit.ng