Daga Karshe Gwamna Zulum Ya Fadi Dalilin Kai Harin Kunar Bakin Wake a Borno

Daga Karshe Gwamna Zulum Ya Fadi Dalilin Kai Harin Kunar Bakin Wake a Borno

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi magana kan harin ta'addancin da ƴan ƙunar baƙin wake suka kai a Gwoza
  • Gwamnan ya bayyana harin a matsayin wani zagon ƙasa ga shirin da yake yi na mayar da ƴan gudun hijira zuwa gidajensu
  • Ya jajantawa iyalan waɗanda suka ransu tare da ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙari wajen kare lafiya da dukiyoyi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi magana kan hare-haren ƙunar baƙin wake da aka kai a garin Gwoza na jihar.

Gwamna Zulum ya bayyana hare-haren a matsayin wani aikin zagon ƙasa domin daƙile shirin sake mayar da ƴan gudun hijira zuwa gidajensu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Yobe ya rantsar da sababbin kwamishinoni da hadimai, ya ba su shawara

Zulum ya magantu kan harin bam a Borno
Gwamna Zulum ya yi magana kan harin kunar bakin wake a Borno Hoto: @govborno
Asali: Facebook

Gwamna Zulum ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ya isa Maiduguri babban birnin jihar a ranar Asabar bayan ya kwashe kwanaki 35 ba ya jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kwanakin baya ne dai ƴan ƙunar baƙin wake guda huɗu suka kashe sama da mutane 32 sannan wasu 48 suka samu raunuka daban-daban.

Me Zulum ya ce kan harin bam a Borno?

Ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da sojoji da sauran jami’an tsaro domin inganta tsaron lafiyar jama’a, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Abin baƙin ciki ne abin da ya faru a garin Gwoza, ya zo ne a lokacin da muke murnar ficewar mayaƙan Boko Haram a jihar Borno."
"Mun ga jerin hare-haren ƙunar baƙin wake a Gwoza wanda na yi amanna aikin zagon ƙasa ne a wannan lokacin saboda muna ƙoƙarin yadda za mu mayar da mutane matsugunansu, sannan ina tunanin wasu ba su son hakan."

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi shirin Tinubu kan ceto 'yan Najeriya daga halin matsi

- Farfesa Babagana Umara Zulum

"Ina kira ga mutanen Gwoza da su kwantar da hankulansu su zama masu bin doka da oda ta hanyar haɗa kai da gwamnatin jiha da nufin tabbatar da cewa an mayar da ƴan gudun hijira gidajensu na asali.

Gwamna Zulum ya kuma buƙaci jama'a da su ƙara haƙuri kan halin matsin tattalin arziƙi da matsalar tsaro a jihar.

Tinubu ya yi Allah wadai da harin bam a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-haren bama-bamai da suka haddasa asarar rayuka da raunata wasu mutane da dama a ƙaramar hukumar Gwoza da ke jihar Borno.

Hare-haren na ƙunar baƙin wake sun hallaka aƙalla mutane 18 tare da raunata wasu da dama a ranar Asabar, 29 ga watan Yulin 2024 a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng