Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar CCT da Wasu Hukumomi 6
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe na shugabanni a wasu hukumomin gwamnatin tarayya
- Shugaban ƙasan ya amince da naɗin Dakta Mainasara Umar Kogo a matsayin sabon shugaban hukumar CCT
- Bayan naɗin Mainasara Umar Kogo, Shugaba Tinubu ya kuma amince da naɗin sababbin shugabannin wasu hukumomin gwamnati guda shida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin Dakta Mainasara Umar Kogo a matsayin shugaban hukumar ɗa'ar ma'ikata (CCT).
Shugaban ƙasan ya amince da naɗin ne na Mainasara a matsayin sabon shugaban hukumar CCT a ranar Asabar, 13 ga watan Yulin 2024.
Hukumar CCT ta yi sabon shugaba
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasan, Ajuri Ngelale, ya fitar a shafinsa na Facebook, a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakta Mainasara gogaggen lauya ne kuma mai sharhi a fannin shari'a, tsaro, tattalin arziƙi, siyasa da diflomasiyyar ƙasa da ƙasa.
Shugaba Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe
Shugaban ƙasan ya kuma amince da naɗin shugabannin wasu hukumomin gwamnati guda shida, cewar rahoton jaridar Tribune.
Sauran hukumomin da aka naɗa musu sababbin shugabanni sun haɗa da hukumar NIHSA, hukumar NDE, hukumar NLTF, hukumar NAGGW, hukumar NPC da hukumar NSITF.
Shugaba Tinubu ya naɗa Umar Ibrahim Mohammed, a matsayin sabon darakta janar na hukumar NIHSA.
Shugaban ƙasan ya kuma amince da naɗin Mista Silas Agara a matsayin darakta janar na hukumar NDE.
Haka kuma shugaban ƙasan ya naɗa Mista Tosin Adeyanju a matsayin shugaban hukumar NLTF.
Shugaba Tinubu ya kuma amince da naɗin Saleh Abubakar a matsayin darakta janar na hukumar NAGGW.
Shugaban ƙasan ya kuma amince da naɗin Baffa Dan Agundi a matsayin darakta janar na hukumar NPC.
Hakazalika Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Mista Oluwaseun Faleye a matsayin sabon shugaban hukumar NSITF.
Tinubu ya ba surikin Ganduje muƙami
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya naɗa Idris Ajimobi wanda suriki ne a wajen Abdullahi Umar Ganduje a matsayin hadimi na musamman.
Shugaba Tinubu ya naɗa Idris Ajimobi a matsayin hadiminsa a ɓangaren ci gaba da kula da kiwon dabbobi a Najeriya.
Asali: Legit.ng