Sanata Ya Caccaki Ali Ndume Kan Tabo Batun Yunwa a Mulkin Tinubu

Sanata Ya Caccaki Ali Ndume Kan Tabo Batun Yunwa a Mulkin Tinubu

  • Kalaman Sanata Ali Ndume kan halin yunwa da ake ciki a ƙasar nan ba su yiwa Sanata Sunday Karimi daɗi ba
  • Sanatan ya caccaki Ali Ndume inda ya buƙace da ya daina furta kalamai masu kaushi kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Ya bayyana cewa a lokacin mulkin Muhammadu Buhari ba a riƙa jin ɗuriyar Ndume ba yana caccakar gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata Sunday Karimi mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa, ya gargadi Sanata Ndume.

Sanatan ya buƙaci Ali Ndume da ya guji furta munanan kalamai ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sunday Karimi ya caccaki Ali Ndume
Sanata Sunday Karimi ya caccaki Ali Ndume kan sukar Tinubu Hoto: Hon. Sunday Karimi 4 Senate, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sen Mohammed Ali Ndume
Asali: Facebook

Me Sanata Ali Ndume ya ce kan Tinubu?

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi magana bayan gini ya hallaka ɗalibai sama da 20 a Arewa

Sanatan na Kogi ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan iƙirarin Sanata Ali Ndume na cewa Tinubu ya yi tsit a fadar shugaban ƙasa ba tare da sanin halin da ƴan Najeriya ke ciki ba, cewa rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan dai za a iya tunawa Sanata Ali Ndume ya nuna damuwa kan tsadar rayuwa da ƙarancin abinci da ake fama da shi a ƙasar nan.

Sunday Karimi ya caccaki Ndume

Da yake martani kan kalaman na Ndume, Sanata Sunday Karimi ya bayyana damuwarsa kan ɗabi'ar da mai tsawatarwar na majalisar dattawa yake nunawa, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Ya nuna cewa mafi yawan sukar da Sanata Ndume ke yi wa gwamnatin Tinubu da alama sun samo asali ne daga wata manufa ta kashin kansa domin ganin ya ɓata gwamnati ko ta halin ƙaƙa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya gamu da babban matsala a Kano, sanata ya fice daga jam'iyyar APC

Sanatan na Kogi ya nuna cewa Ali Ndume ya yi shiru lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari saboda ya fito daga Arewacin Najeriya.

"Yawancin zarge-zargen Sanata Ndume ba su da ƙwaƙƙwarar hujja kuma suna da nasaba da son ganin bayan gwamnati ba wai domin kawo gyara ba."
"A matsayinsa na gogaggen ɗan majalisa wanda ya kwashe sama da shekaru 20 a majalisar tarayya, ya kamata Sanata Ndume ya yi taka-tsan-tsan a kalamansa tare da kaucewa furta kalaman da za su ƙara dagula al’amuran siyasa da raba kan al’umma."

- Sanata Sunday Karimi

Tinubu zai magance halin matsi a ƙasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya faɗi shirin shugaban ƙasa Bola Tinubu kan halin matsin rayuwa da ake fama da shi a ƙasar nan.

Gwamnan ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ƙudiri aniyar yin iyakacin bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya fitar da Najeriya daga halin da take ciki domin yin gogayya da ƙasashen da suka ci gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng