Gwamna Ya Rufe Makarantar Sakandire Bayan Mutuwar Ɗalibai 22, Ya Ɗauki Mataki

Gwamna Ya Rufe Makarantar Sakandire Bayan Mutuwar Ɗalibai 22, Ya Ɗauki Mataki

  • Gwamnan jihar Filato ya rufe makarantar sakandiren da gini ya rufta kan ɗalibai ana tsaka da rubuta jarabawa a Jos
  • Bayanai sun nuna cewa rugujewar ginin ta yi ajalin mutane sama da 20 yayin da wasu 132 suka samu raunuka
  • Yayin da ya kai ziyara harabar makarantar Saint Academy, gwamnan ya ce za a gudanar da binciken kan gine-ginen sauran makarantu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya sanar da rufe makarantar sakandire ta Saint Academy nan take bayan ruftawar gini ranar Jumu'a.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a gudanar da bincike mai zurfi kan ibtila'in rugujewar ginin makarantar wanda ya yi sanadin mutuwar ɗalibai 22 da raunata wasu 132.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi magana bayan gini ya hallaka ɗalibai sama da 20 a Arewa

Gwamna Caleb Mutfwang.
Gwamnan Filato ya garƙame makarantar da gini ya kashe mutane a Jos Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Gwamnan ya bada umarnin rufe makarantar ne a lokacin da ya ziyarci harabar ginin da ya ruguje domin tantance halin da ake ciki, kamar yadda Channels tv ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin ziyarar Gwamna Mutfwang ya zagaya harabar makarantar tare da shugabanta da wasu malamai da suka zo domin tarbarsa.

Idan baku manta ba Legit Hausa ta kawo rahoton yadɗa ginin makarantar ya danne ɗalibai da malamai kusan 200 ana tsaka da jarabawa ranar Jumu'a.

Gwamnatin Filato ta tabbatar da cewa mutum 22 sun mutu yayin da wasu sama da 100 ke kwance ana kula da su a asibitoci daban-daban a Jos, rahoton Vanguard.

Wane mataki Gwamna Mutfwang ya ɗauka?

Da yake jawabi kan matakin da ya ɗauka a lokacin ziyarar, gwamnan Filato ya ce:

"Abin da ya faru abun takaici ne saboda haka mun rufe makarantar nan take. Ba zamu lamunci sakaci ba kuma wannan zai zama tamkar saƙon gargaɗi ga sauran makarantun kuɗi.

Kara karanta wannan

Mutum 22 sun mutu sakamakon mummunan ibtila'in da ya afka wa ɗalibai a Arewa

"Ba zai yiwu neman kuɗi ya shiga gaban tsare rayukan al'umma ba, don haka zamu fara gudanar da bincike kan sauran makarantu, zamu gwada ƙwarin gine-ginensu don tabbatar da cewa mutane za su shiga ba tare da fargaba ba."

Tinubu ya jajantawa mutanen Jos

A wani rahoton kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon ta'azziyya ga iyalan waɗanda suka rasu sakamakon ruftawar ginin wata makaranta a jihar Filato.

Shugaban ƙasar ya kuma jajantawa duka waɗanda lamarin ya rutsa da su inda ya bayyana kifewar ginin a matsayin babban rashi ga ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262