Gwamnan Yobe Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni da Hadimai, Ya Ba Su Shawara

Gwamnan Yobe Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni da Hadimai, Ya Ba Su Shawara

  • Jihar Yobe ta samu ƙarin sabbabin kwamishinoni guda biyu da masu ba da shawara na musamman ga gwamnan jihar mutum 28
  • Gwamna Mai Mala Buni ya rantsar da sababbin masu riƙe da muƙaman domin fara sauke nauyin da aka ɗora musu
  • Ya buƙace su da su yi aiki tuƙuru domin ganin ba da tasu gudunmawar wajen kawo ci gaba ga al'ummar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya rantsar da kwamishinoni biyu, shugaban ma’aikata, manyan sakatarori guda huɗu a jihar.

Gwamnan ya kuma rantsar da masu ba da shawara na musamman guda 28 domin gudanar da ayyuka masu inganci a jihar.

Gwamna Buni ya rantsar da kwamishinoni
Gwamnan Yobe ya rantsar da sababbin kwamishinoni Hoto: Mai Mala Buni
Asali: Twitter

Wace shawara ya ba su?

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi magana bayan gini ya hallaka ɗalibai sama da 20 a Arewa

Gwamna Buni ya buƙaci sababbin kwamishinonin da su bayar da tasu gudunmawar wajen tsarawa da aiwatar da dukkanin manufofi da tsare-tsare da ayyuka na gwamnati cikin gaskiya domin amfanin al’ummar jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma buƙace su da su yi amfani da ƙwarewar da suke da ita wajen ƙara nasarorin da gwamnatin jihar ta samu, cewar rahoton jaridar Leadership.

Sababbin kwamishinonin da aka rantsar sun haɗa da Alhaji Mohammed Mohammed Bara da Farfesa Abba Idris, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

"Ana sa ran ku yi amfani da ƙwarewarku gogewa wajen kawo sababbin dabaru domin ƙara ƙima ga nasarorin da wannan gwamnatin ta samu."
"Ya kamata ku fifita yiwa jama’a hidima tare da la’akari sosai ga makomar jihar."

- Mai Mala Buni

Gwamnan ya buƙaci sabon shugaban ma’aikata, Hamidu M. Alhaji, da ya samar da jajirtattun ma'aikata masu inganci domin yiwa jihar aiki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban kwaleji, sun bukaci a ba su N70m

Ya buƙaci masu ba da shawara na musamman da su riƙa tuntuɓar mutanen yankinsu domin tabbatar da cewa ana damawa da su a cikin harkokin mulki.

Gwamna Buni ya dakatar da ciyaman

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina, Idrissa Mai Bukar Machina.

Gwamna Mai Mala Buni ya dakatar da shugaban ƙaramar hukumar ne bisa zargin rashin ɗa'a da rashin biyayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng