Gwamna Ya Fadi Shirin Tinubu Kan Ceto 'Yan Najeriya Daga Halin Matsi

Gwamna Ya Fadi Shirin Tinubu Kan Ceto 'Yan Najeriya Daga Halin Matsi

  • Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja
  • Gwamnan ya bayyana cewa shugaban ƙasan a shirye yake wajen ganin ya magance matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙi a ƙasar nan
  • Inuwa Yahaya ya bayyana cewa yana ƙoƙari wajen ganin ya magance matsalar rashin tsaro a Gombe domin bunƙasa ayyukan noma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya faɗi shirin shugaban ƙasa Bola Tinubu kan halin matsin rayuwa da ake fama da shi a ƙasar nan.

Gwamnan ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ƙudiri aniyar yin iyakacin bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya fitar da Najeriya daga halin da take ciki domin yin gogayya da ƙasashen da suka ci gaba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi magana bayan gini ya hallaka ɗalibai sama da 20 a Arewa

Gwamnan Gombe ya gana da Tinubu
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce Tinubu na shirin magance halin matsi a kasa Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa a ranar Juma’a, bayan wata ganawa da Shugaba Tinubu, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Gwamna Inuwa ya tattauna da Tinubu a kai?

Ya ce ya je fadar shugaban ƙasa ne domin ya gana da shugaban ƙasa kan abubuwan da ke faruwa a ƙasar nan musamman ta fuskar tattalin arziƙi da samar da abinci.

"Mun tattauna sosai. Mun yi magana kan dukkanin batutuwan, sannan ina da tabbacin shugaban ƙasa a shirye yake kuma yanayin iyakar bakin ƙoƙarinsa."

- Inuwa Yahaya

Gwamnan ya bayyana cewa jihar Gombe na magance matsalar rashin tsaro domin tabbatar da an samu ƙarin abincin da ake nomawa, rahoton jaridar The Sun ya tabbatar.

"Muna yin bakin ƙoƙari dangane da batun rashin tsaro. Abin takaici ne cewa ƙasar nan musamman yankin Arewa maso Gabas ya yi fama fiye da shekara 15 da matsalar ƴan Boko Haram, rashin tsaro da raba mutane da gidajensu"

Kara karanta wannan

NLC Vs Tinubu: Ministoci 2 sun bayyana Lokacin da za a warware batun ƙarin albashi

- Inuwa Yahaya

Tinubu zai yiwa ministoci garambawul

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon na hannun daman Atiku Abubakar ya yi martani kan Ministocin Shugaba Bola Tinubu.

Daniel Bwala ya ce nan da ƴan kwanaki kadan Tinubu zai yi garambawul a mukaman ministocinsa domin kawo gyara kan yadda ake gudanar da al'amura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng