Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Yi Watsi da Tsarin da El Rufai Ya Kawo a Jihar

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Yi Watsi da Tsarin da El Rufai Ya Kawo a Jihar

  • Majalisar dokokin jihar Kaduna ta yiwa dokar zaɓe ta jihar garambuwal inda ta soke tsarin amfani da na'ura wajen gudanae da zaɓe
  • Majalisar ta amince da ƙudirin doka wanda zai sanya a koma amfani da akwtunan zaɓe da ƙuri'u wajen yin zaɓe a jihar
  • A lokacin tsohon gwamnan jihar Nasir Ahmad El-Rufa an yi doka wacce ta kawo tsarin gudanar da zaɓe ta hanyar amfani da na'urar kaɗa ƙuria

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da ƙudirin dokar yiwa dokae zaɓen jihar ta shekarar 2021 garambawul.

Majalisar ta amince da ƙudirin dokar wanda ya share yin amfani da na'urar kaɗa ƙuri'a wajen gudanar da zaɓe.

Kara karanta wannan

Daga karshe Gwamna Zulum ya fadi dalilin kai harin kunar bakin wake a Borno

Majalisa ta soke tsarin da El-Rufai ya kawo a Kaduna
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta soke dokar amfani da na'ura wajen zabe Hoto: @ubasanius, @elrufai
Asali: Twitter

An daina amfani da na'ura wajen zaɓe a Kaduna

Kakakin majalisar, Yusuf Dahiru Liman, ya zartar da dokar bayan amincewa da cikakken rahoto kan dokar da aka yiwa kwaskwarima wanda shugaban kwamitin majalisar kan harkokin shari’a, Emmanuel Kantiok ya gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bisa sabuwar dokar, za a riƙa amfani da rajistar masu kaɗa ƙuri'a wajen tantancewa da kaɗa ƙuri'a, cewar rahoton jaridar Leadership.

Sannan hukumar zaɓe za ta riƙa samar da ƙuri'u da akwatunan zaɓe domin gudanar da zaɓe, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Meyasa aka sauya dokar?

Bayan kammala zaman majalisar, mataimakin shugaban kwamitin kuma mamba mai wakiltar Zaria, Ismail Lawal, ya bayyana cewa ana buƙatar gyaran ne saboda zaɓen ƙananan hukumomi ya kusa.

"Za mu koma bin hanyar da muke yin amfani da ita wajen yin zaɓe a baya, inda za a kawo akwatunan zaɓe da ƙuri'u. Muna son jama'a su fahimci cewa za a yi zaɓe cikin gaskiya da adalci."

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci a ƙarar da aka nemi tsige Gwamnan PDP

- Ismail Lawal

A baya dai majalisar ta tabbatar da naɗin Halima Sani, Abubakar Musa da Ahmed Yahya a matsayin kwamishinonin dindindin na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna (KADSIECOM).

An samu koma baya

Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin jihar Kaduna mai suna Isah Lawal, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa kan wannan matakin da majalisar ta ɗauka.

Ya bayyana cewa sauka daga kan tsarin yin amfani da na'ura wajen yin zaɓen koma baya ne, domin za a koma tafka maguɗi ne kawai.

"Wannan koma baya ne gaskiya domin yanzu za a koma tafka maguɗi yayin zaɓe kuma gwamna zai riƙa ɗora ƴan amshin shatansa ne kawai, saboda ba za a yi sahihin zaɓe ba."

- Isah Lawal

El-Rufai ya caccaki Gwamna Uba Sani

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake caccakar magajinsa, Gwamna Uba Sani na jihar.

El-Rufai ya caccaki Uba Sani ne bisa zargin haɗa ƙarya da ƙarairayi wajen zargin gwamnatinsa da karkatar da maƙudan kuɗaɗen da suka kai N423,115,028,072.88.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng