Mutum 22 Sun Mutu Sakamakon Mummunan Ibtila'in da Ya Afka Wa Ɗalibai a Arewa
- Gwamnatin Filato ta bayyana halin da ake ciki bayan wani ginin makaranta ya danne ɗalibai da malamai a garin Jos ranar Jumu'a
- Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Musa Ashom ya ce a halin da ake cikin mutum 22 sun mutu yayin da wasu 132 ke kwance suna jinya
- Ginin makarantar Saits Academy ya rufta kan ɗalibai ne a lokacin da suke rubuta jarabawar karshen zango na uku a Jos
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau - Mutane 22 ne suka mutu yayin da 132 suka samu raunuka a ginin makarantar da ya ruguje a garin Jos babban birnin jihar Filato a safiyar ranar Juma’a.
Idan baku manta ba mun kawo maku rahoton cewa makarantar sakandare Saints Academy da ke Jos ta kife a lokacin da dalibai ke rubuta jarabawar zango na uku.
Jos: Mutum 22 sun mutu a rugujewar gini
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Hon Musa Ashom ya fitar, ya ce zuwa ƙarfe 6:00 na yammacin Jumu'a adadin wadanda suka mutu ya kai 22
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Daily Trust ta kawo, Hon Ashom ya bayyana cewa ma'aikatan agaji sun yi nasarar ciro ɗalibai da malaman da lamarin ya shafa mutum 154.
"A halin da ake ciki yanzu misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Juma'a, an ceto mutane 154 daga baraguzan ginin, abin alhinin shi ne 22 daga ciki sun mutu.
"Ɗalibai da malaman makarantar da ibtila'in ya afka wa suna karɓan kulawa a asibitoci daban-daban a birnin Jos. A asibitin kwararru na Filato an kwantar da mutum 39, daga ciki 3 sun mutu.
“A Asibitin OLA kuma an kai mutum 32 amma biyar daga ciki sun mutu. Bayanai daga Asibitin Koyarwa na Jami'ar Bingham sun nuna an kai ɗalibai 55 yayin da 14 sun mutu."
- Hon Musa Ashom.
Wane mataki gwamnatin Filato ta ɗauka?
Gwamnatin Jihar Filato ta bayar da umarnin kai agajin gaggawa nan take bayan samun labarin ruftawar ginin makarantar kan ɗalibai da malamai kusan 200.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da ta jiha (SEMA), jami'an tsaro, ƙungiyar Red Cross, da malaman lafiya na aiki tuƙuru don ceto waɗanda lamarin ya shafa.
Gwamna Barista Caleb Mutfwang ya ba da umarni ga asibitoci da su dauki nauyin duk wadanda rugujewar ta shafa ba tare da jiran biyan wasu kuɗaɗe ba, Vanguard ta rahoto.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan ibtila'in akwai sakacin masu makarantar saboda ginin ya tsage tun ba yanzu ba amma suka ci gaba da aiki da shi.
Mutumin mai suna Muhammed Ahmed ya yi kira ga Gwamna Mutfwang ya ɗauki mataki mai tsauri kamar tilasta masu biyan diyya.
Ya ce:
"Abin da ya faru ya tada mana hankali, tun kwanakin baya mutane sun yi ƙorafin cewa ginin ya nuna shaidar zai iya rugujewa amma aka ci gaba da karatu a ciki.
"Ni ina ganin bai kamata gwamnan mu ya sassauta masu ba, a ɗauki mataki mai tsauri idan ta kama a umarci su biya mutane diyya domin akwai ganganci a lamrin."
Ɗalibai 200 sun makale a Jos
A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Filato ta ce ɓangaren da ya ruguje a makarantar sakandiren Saints Academy yana ɗauke da ɗalibai kusan 200.
Kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar, Musa Ashoms ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara makarantar ranar Jumu'a.
Asali: Legit.ng