Bayan Hukuncin Kotun Koli, Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule da Gwamnonin Najeriya, Bayanai Sun Fito

Bayan Hukuncin Kotun Koli, Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule da Gwamnonin Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawar sirri da gwamnonin Najeriya a fadarsa da ke Aso Rock a birnin tarayya Abuja
  • Ganawar shugaban ƙasan da gwamnonin na zuwa ne bayan Kotun Ƙoli ta yi hukunci wanda ya ba ƙananan hukumomin ƴancin cin gashin kansu
  • Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da gwamnonin ne bayan ya kammala wata ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ganawa da wasu gwamnoni a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.

Taron na zuwa bayan hukuncin da Kotun Ƙolin ta yanke na tabbatar da ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, 'yan kwadago sun bayyana matsayarsu kan mafi karancin albashi

Tinubu ya sa labule da gwamnoni
Shugaba Tinubu ya gana da gwamnoni Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce taron ya fara ne bayan Shugaba Tinubu ya gana da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wa suka halarci taron Tinubu da gwamnoni?

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima yana daga cikin halartar taron wanda ake gudanarwa a fadar shugaban ƙasa.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara; Charles Soludo na Anambra da Usman Ododo na Kogi.

Duk da dalilan yin taron ba su bayyana ba, alamu na nuna cewa taron baya rasa nasaba da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Kotun Ƙoli ta yi hukunci

Kotun Ƙolin dai ta yanke hukuncin cewa gwamnatin tarayya ta riƙa biyan ƙananan hukumomi kuɗadensu kai tsaye zuwa asusunsu daga asusun gwamnatin tarayya.

Ta kuma hana gwamnonin jihohi 36 na ƙasar nan tsige zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi daga kan muƙamansu.

Kara karanta wannan

An tura dan TikTok zuwa gidan yari saboda zagin shugaban kasa

Gwamnatin tarayya ce ta kai ƙarar gwamnonin a gaban Kotun Ƙoli domin nemawa ƙananan hukumomin ƴancin cin gashin kansu.

Dogarin Tinubu ya samu sarauta

A wani labarin kuma, kun ji cewa an naɗa dogarin shugaban ƙasa Bola Tinubu, Laftanal kanal Nurudeen Alowonle Yusuf a matsayin sabon Sarkin Ilemona, hedikwatar karamar hukumar Oyun a jihar Kwara.

Duk da masu nada sarkin basu sanar da hakan ba a hukumance, wani fitaccen shugaban al'ummar yankin wanda ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar da nadin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng