Ana Cikin Batun Yunwa a Kasa Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sababbin Wadanda Ya Ba Mukamai

Ana Cikin Batun Yunwa a Kasa Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sababbin Wadanda Ya Ba Mukamai

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta tarayya a karo na 14 tun bayan da aka ƙaddamar da ita
  • Kafin fara zaman, Shugaba Tinubu ya rantsar da manyan sakatarori takwas na tarayya domin fara sauke nauyin da ya rataya a wuyansu
  • Manyan sakatarorin dai sun fito ne daga jihohi daban-daban na ƙasar nan inda za su maye gurbin waɗanda suka bar aiki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zartaswa ta tarayya a fadarsa da ke Abuja.

Shugaban ƙasan ya rantsar da manyan sakatarori na tarayya guda takwas kafin fara zaman majalisar zartaswar.

Tinubu ya rantsar da manyan sakatarori
Tinubu ya rantsar da manyan sakatarori takwas na tarayya Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Manyan sakatarorin sun yi rantsuwar kama aiki ne daf da fara taron majalisar zartaswar da ke gudana a fadar gwamnati da ke Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki matakin magance yunwar da ake yi a kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron majalisar zartarwar na gwamnatin tarayya dai shi ne karo na 14 tun bayan kaddamar da majalisar a ranar 28 ga watan Agusta, 2023.

Tinubu ya rantsar da manyan sakatarori

Takaitaccen taron rantsarwar wanda aka gudanar a rukuni biyu, ya kasance ƙarƙashin jagorancin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale.

Manyan sakatarorin da aka rantsar sun haɗa da Dakta Emanso Okop (Akwa-Ibom), Obi Vitalis (Anambra), Mahmood Fatima (Bauchi) da Danjuma Sanusi (Jigawa).

Sauran sune Olusanya Olubunmi (Ondo), Dakta Keshinro Ismaila (Zamfara), Akujobi Ijeoma (Kudu maso Gabas), da Isokpunwu Osaruwanmwen (Kudu maso Kudu).

An taya Tinubu murna samun muƙami

Ƴan majalisar zartaswar sun kuma taya Shugaba Tinubu murnar sake zaɓensa a matsayin shugaban ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS), rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Sakataren gwamnatin tarayya wanda ya yi magana a madadin ƴan majalisar ministocin ya ce shugabannin yankin Afirka ta Yamma sun ga jajirtaccen jagora a Tinubu wanda hakan ya sanya suka yanke shawarar sake zaɓensa.

Kara karanta wannan

Shugabancin ECOWAS: Amfanin da Najeriya za ta samu sakamakon sake zaben Tinubu

Dalilin sanya sakatarori durƙusawa Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya magantu bayan ce-ce-ku-ce kan durkusawa da manyan sakatarori suka yiwa Bola Tinubu.

Nyesom Wike ya ce shi ya ba su umarnin durƙusawa saboda irin karamci da shugaban ƙasan ya yi musu a ma'aikatar Abuja (FCTA).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng