Majalisar Wakilai Ta Hana Tinubu Aiwatar da Yarjejeniyar Samoa? Gaskiya ta Bayyana
- Majalisar wakilai ta yi magana kan rahotannin da ke cewa ta buƙaci gwamnaton tarayya da dakatar da aiwatar da yarjejniyar Samoa
- Kakakin majalisar, Honarabul Akintunde Rotimi, ya bayyana cewa majalisar ta yi nazari sosai kan yarjejeniyar ta Samoa
- Akintunde Rotimi bayyana cewa majalisar ba buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da yarjejeniyar ba ko aiwatar da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta yi magana kan batun neman gwamnatin taraya ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar Samoa.
Majalisar ta musanta cewa ta amince da ƙudirin da ya buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar Samoa.
Kakakin majalisar, Honorabul Akintunde Rotimi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me majalisa ta ce kan yarjejeniyar Samoa?
Ya bayyana cewa ƙudirin da majalisar ta amince da shi ne na bincikar sharuɗɗa masu cece-kuce da ke cikin yarjejeniyar domin tabbatar da cewa sun yi daidai da dokoki, kundin tsarin mulki da ɗabi'un ƙasar nan.
Rotimi ya bayyana cewa majalisar ta buƙaci gwamnatin tarayya ta tabbatar ta tattauna da masu ruwa tsaki kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar.
"A yayin muhawarar, an nuna damuwa game da wasu sharuddan da ake zargin suna tilasta goyon bayan auren jinsi a matsayin sharaɗin samun tallafin kuɗi da sauran tallafi daga ƙasashen da suka ci gaba."
"Yana da kyau a bayyana cewa majalisar wakilai ba ta cimma ƙudirin neman dakatar da yarjejeniyar ko dakatar da aiwatar ita kamar yadda wasu gidajen jaridu suka ruwaito cikin kuskure."
"A maimakon hakan, majalisar ta yanke shawarar yin nazari sosai kan sharuɗɗan da ke cikin yarjejeniyar Samoa ta hanyar zaman majalisa."
- Akintunde Rotimi
Malamai sun gargaɗi Tinubu kan yarjejeniyar Samoa
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar malamai da limaman Musulunci a jihar Kaduna sun yi martani kan yarjejeniyar Samoa.
Majalisar malaman ta yi Allah wadai da yarjejeniyar inda ta gargadi shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu game da sanya hannu kan tsarin.
Asali: Legit.ng