Ba a Gama da Betta Edu Ba, Majalisa Ta Titsiye Ministar Tinubu Kan Badakalar N1.5bn

Ba a Gama da Betta Edu Ba, Majalisa Ta Titsiye Ministar Tinubu Kan Badakalar N1.5bn

  • Majalisar wakilai ta gayyato ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanaye ta bayyana a gabanta kan wasu zarge-zarge
  • Kwamitin majalisar mai kula da harkokin mata ya zauna da ministar inda ya yi mata tambayoyi kan badaƙalar N1.5bn na kuɗaɗen ƴan kwangila
  • Zaman kwamitin da ministar dai ya tashi baram-baram bayan ta yi zargin ba a yi mata adalci ba kan tambayoyin da ake yi mata

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin mata da ci gaban jama’a, ya titsiye ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohaneye, kan rashin biyan ƴan kwangila N1.5bn bayan fitar da kuɗaɗen.

Kwamitin na binciken zargin karkatar da N1.5bn domin biyan ƴan kwangila bayan ya samu takardar koke daga ƴan kwangilar kan rashin biyan kuɗin kwangilar da suka yi wa ma’aikatar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki matakin magance yunwar da ake yi a kasa

Majalisa ta titsiye ministar mata, Uju Kennedy-Ohaneye
Majalisa ta yiwa ministar harkokin mata tambayoyi kan badakalar N1.5bn Hoto: Uju Kennedy-Ohaneye, @houseNGR
Asali: UGC

Kwamitin dai a zamansa na ƙarshe ya gayyaci ministar da ta gurfana a gabansa domin bayyana dalilin rashin biyan kuɗaɗen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta titsiye ministar Tinubu

Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ba a biya ƴan kwangilar kuɗaɗensu ba, ministar ta ce ba a ba ma’aikatar kuɗaɗen ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Sai dai, kwamitin ya yi watsi da iƙirarin nata, inda ya ce tun da farko daraktan kudi da asusu ya tabbatar da fitar da kuɗaɗen.

A nasa ɓangaren, daraktan kuɗi da asusu, Aloy Ifeakandu, ya ce kaso 25% cikin 100% na kuɗaɗen kwangilar ne aka ba ma’aikatar.

Kwamitin, yayin da yake bibiyar takardun da ma’aikatar ta gabatar, ya nemi jin ba'asi kan N45m da aka ce an kashe wajen shirya bikin sabuwar shekara ga yara da N20m domin siyan sabulu ga jariran da aka haifa a ranar sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun ba gwamnan PDP sabon wa'adi kan kasafin kudin 2024

Kwamitin ya kuma nuna rashin gamsuwa kan N1.5m da ta ce ta kashe wajen sanya man fetur a motoci a wata tafiya zuwa jihar Anambra, amma ministar ta bayar da hujjar kashe kuɗaɗen, rahoton tashar TVC ya tabbatar.

An tashi baram-baram

A yayin da kwamitin ya ci gaba da tono wasu laifuffukan da ake zargin ma’aikatar ta yi, lamarin ya koma ce-ce-ku-ce tsakanin ministar da kwamitin, inda ta ci gaba da ɗaga murya, tana mai zargin ba a yi mata adalci.

Shugabar kwamitin, Kafilat Ogbara, wacce ta ya bayyana halayyar ministar a matsayin rashin kunya da cin mutunci ga majalisar, ta ɗage zaman har sai baba ta gani.

Ta ce kwamitin zai kai rahoto ga majalisar cewa ministar ta ƙi ba da haɗin kai kuma ba ta ganin mutuncin majalisar.

Majalisar wakilai ta gargaɗi Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar Samoa wacce ta jawo cece-kuce a ƙasar nan.

Majalisar ta kuma yanke shawarar bincikar yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayya ta sanya wa hannu a ranar 28 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng