'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2 da Sace Wasu da Dama a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2 da Sace Wasu da Dama a Kaduna

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hare-hare a wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna
  • Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun sace mutum 19 a ƙauyen Maraban Walijo bayan sun kai wani farmaki amma mutanen ƙauyen sun hallaka ɗan bindiga ɗaya
  • Daga baya ƴan bindigan sun dawo ɗaukar fansa amma jami'an tsaro sun hana su shiga ƙauyen, sai suka shiga wanda yake makwabtaka da shi suka hallaka mutum biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun hallaka mutum biyu a ƙauyen Dagwarga da ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutum 19 a ƙauyen Maraban Walijo wanda yake makwabtaka da Dagwarga.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sanye da kayan mata sun sace mutane masu yawa a Katsina

'Yan bindiga sun hallaka mutum biyu a Kaduna
'Yan bindiga sun sace mutum 19 a jihar Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka kai hari a Kaduna

Wani mazaunin ƙauyen Dagwarga, Alhaji Abdullahi Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Daily Trust a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa harin da ƴan bindigan suka kai a Dagwarga ya yi kama da harin ramuwar gayya.

"Ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen Maraban Walijo a ranar Lahadi inda suka sace mutum 19. A yayin harin, mutanen garin sun kashe ɗan bindiga ɗaya."
"Sun dawo ranar Litinin domin ɗaukar fansa, amma saboda akwai jami'an tsaro masu yawa a Maraban Walijo, sai suka kai mana hari a Dagwarga wanda baya da nisa da Maraban Walijo."

- Alhaji Abdullahi Abubakar

A cewar Abubakar, maharan sun shigo ƙauyen Dagwarga da misalin ƙarfe 2:00 na dare sannan suka fara harbi kan mai uwa da wabi, inda suka hallaka Alhaji Danlami Goni da Alhaji Auwalu Bawa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yiwa jami'an tsaro kwanton bauna, sun hallaka mutum 4

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba, ASP Mansur Hassan kan aukuwar lamarin.

Kakakin rundunar ƴan sandan bai ɗauki kiran da aka yi masa a waya ba kuma bai biyo ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan bindiga sun sace ƴan jarida

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan jarida biyu da iyalansu a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kai farmaki ƙauyen Danhonu da ke garin Millennium City inda suka shiga gidajen ƴan jaridar guda biyu sannan suka sace su tare da matansu da ƴaƴansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng