Majalisa Ta Jawo Hankalin Tinubu Kan Yunwa a Kasa, Ta Ba Shi Mafita
- Majalisar dattawan Najeriya ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da ya gaggauta magance matsalar ƙarancin abinci a ƙasar nan
- Hakan na zuwa ne bayan ƙudirin da Sanata Sunday Karimi ya gabatar kan matsalar ƙarancin abinci da hauhawar farashin kayayyi a ƙasar nan
- Ƙudirin ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta yi da gaske wajen magance matsalin ƙarancin abinci, garkuwa da mutane da ta'addanci a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta buƙaci shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta magance matsalar ƙarancin abinci a faɗin ƙasar nan.
Hakan na zuwa ne biyo bayan ƙudirin da Sunday Karimi (APC, Kogi ta Yamma) ya gabatar kuma Ali Ndume (APC, Borno ta Kudu) ya marawa baya a zauren majalisar ranar Talata.
An jawo hankalin Tinubu kan yunwa a ƙasa
Ƙudirin ya nuna cewa a cikin ƴan watannin da suka gabata, farashin kayayyaki da kayan masarufi sun yi tashin gwauron zaɓi a ƙasar nan, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanda hakan ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki, rage ƙarfin sayen kayayyaki, da kuma taɓarɓarewar yanayin rayuwa na galibin ƴan Najeriya.
Jaridar Vanguard ta ce Sunday Karimi ya ce sababbin bayanai da hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta fitar sun nuna cewa hauhawar farashin abinci ya ƙaru zuwa kaso 40.66% a shekara, wanda hakan ya ƙaru daga kaso 24.82 da aka samu a watan Mayun 2023.
"Duk ƙoƙarin da gwamnatin tarayya mai ci a yanzu ke yi na magance hauhawar farashin kayan abinci bai haifar da ɗa mai ido ba."
"Akwai buƙatar a yi da gaske wajen magance matsalar ƙarancin abinci, da magance rikicin manoma da makiyaya, da yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, da ta’addanci."
- Sunday Karimi
Wace buƙata majalisar ta nema?
Da yake yin na sa tsokacin, shugaban majalisar dattawa, GodsWill Akpabio, ya bayyana cewa karancin abinci ya biyo bayan rashin tsaro da ya addabi ƙasar nan.
Daga nan ne majalisar dattawan ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta magance matsalar karancin abinci a faɗin ƙasar nan.
Majalisar dattawa za ta binciki aikin Mambilla
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta ɗauki sabon mataki kan aikin wutar Mambila da aka warewa makudan kuɗi.
Majalisar ta umarci kwamiti mai lura da harkar makamashi da kuɗi ya fara bincike kan yadda aka kashe kuɗi a aikin wutar Mambila ba tare da samar da lantarki ba.
Asali: Legit.ng