Shugabancin ECOWAS: Amfanin da Najeriya Za Ta Samu Sakamakon Sake Zaben Tinubu

Shugabancin ECOWAS: Amfanin da Najeriya Za Ta Samu Sakamakon Sake Zaben Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake zama shugaban ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) a karo na biyu.

An sake zaɓen Shugaba Tinubu matsayin shugaban ƙungiyar ECOWAS a babban taron ƙungiyar karo na 65 da ya gudana a fadar shugaban ƙasar Najeriya dake Abuja a ranar Lahadi, 7 ga watan Yulin 2024.

Tinubu ya zama shugaban ECOWAS
Tinubu ya sake zama shugaban kungiyar ECOWAS Hoto: @ecowas_cedeao
Asali: Twitter

Sake zaɓen da aka yi masa na nufin ya yi tazarce a kan shugabancin ƙungiyar bayan an zaɓe shi matsayin shugaba a karon farko a ranar, 9 ga watan Yulin shekarar 2023, cewar rahoton tashar Channels tv.

Amfanin da Najeriya za ta samu a sake zaben Tinubu a ECOWAS

Kara karanta wannan

Majalisa ta jawo hankalin Tinubu kan yunwa a kasa, ta ba shi mafita

Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen yadda ake tafiyar da al'amura a ƙungiyar ECOWAS da yankin yammacin Afirika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yankin Yammacin Afirika na fama da matsalar rashin tsaro da ayyukan ƴan ta'adda a wasu ƙasashe ciki har da Najeriya da ƙasashen da ke makwabtaƙa da ita kamar su Nijar da Chadi.

Ga wasu daga cikin amfanin da Najeriya za ta samu:

Tsaro da zaman lafiya

A matsayin Tinubu na shugaban ECOWAS ɗaya daga cikin nauyin da ya rataya a wuyansa shi ne tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin, cewar rahoton jaridar BBC Pidgin.

Samun ingantaccen tsaro a yankin Afirika ta Yamma zai taimaki Najeriya wacce ke fama da matsalar rashin tsaro da ayyukan ƴan ta'adda.

Idan akwai tsaro a yankin, Najeriya wacce ke da yawan jama'a, tattalin arziƙinta zai bunƙasa sosai sakamakon samun zaman lafiya da tsaro.

Kara karanta wannan

Rikicin masarauta: An aika gargadi ga Kwankwaso da jam'iyyar NNPP

Shugaba Tinubu zai yi ƙoƙari wajen ganin hakan ya tabbata saboda matsalar rashin tsaro a yankin na shafar tattalin arziƙin Najeriya sosai.

Tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya

Daga cikin nauyin da ya rataya a kan Shugaba Tinubu akwai batun tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasashen da ke cikin ƙungiyar ECOWAS.

Najeriya wacce ta kwashe shekara 25 a kan turbar mulkin dimokuraɗiyya za ta so ta ci gaba da kasancewa madubin dubawa ga sauran ƙasashen yankin ta fuskar mulkin dimokuraɗiyya.

Ci gaba da tabbatar mulkin dimokuraɗiyya a yankin, zai sanya fargabar sojoji su ƙwace mulki a Najeriya za ta ɓace.

Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso waɗanda suka ɓalle daga ƙungiyar ECOWAS na ƙarƙashin mulkin sojoji a halin yanzu.

Wa'adin Tinubu ya ƙare a shugabancin ECOWAS

A wani labarin kuma, kun ji cewa wa’adin shugaban ƙasa Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) ya zo ƙarshe a ranar Lahadi, 7 ga watan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

ASUU ta bayyana abin da zai hana ta shiga yajin aiki a fadin Najeriya

A shekarar 2023, ƙungiyar ECOWAS ta amince da Shugaba Tinubuɓa matsayin shugabanta jim kaɗan bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasan Najeriya.

Wannan mukami ya zo wa Tinubu da gardama sakamakon matsalolin da suka dinga faruwa a wasu kasashen ECOWAS musamman wadanda aka yi juyin mulkin gwamnati a cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng