Yobe: 'Yan Sanda Sun Cafke Basarake Bisa Zargin Hannu a Kisan Wani Bawan Allah

Yobe: 'Yan Sanda Sun Cafke Basarake Bisa Zargin Hannu a Kisan Wani Bawan Allah

  • Jami'an ƴan sanda sun kama wani dagaci bisa zargin hannu a kisan direban motar tarakta a jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem ya ce basaraken ya haɗa matasa suka je gona suka aikata kisan
  • Haka nan kuma ƴan sanda sun kama wasu mutum biyar a yankin Damagum bisa zargin yiwa wani bawan Allah fashin N250,000

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - An zargin Magajin Garin Gazarkuma da ke ƙaramar hukumar Nangere a jihar Yobe da aikata kisan kai.

Dakarun ƴan sanda reshen jihar Yobe sun kama basaraken dan kimanin shekara 65, Mohammed Bulama wanda aka fi sani da Zarma bisa zargin kashe direban motar Tarakta.

Kara karanta wannan

An kama mahaifin da ya daure dansa bayan sun rabu da mahaifiyar yaron

Yan sandan Najeriya.
Yan sanda sun kama basarake da zargin hannu a kisan direba a Yobe Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem, ya tabbatar da kama Magajin Garin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda basaraken ya shiga hannu

Ya ce ƴan sanda sun cafke wanda ake zargin ne bayan ya ɗibi matasa dauke da wukake, sanduna, baka da kibau suka kai farmaki gonar wani Maigari Mato a kauyen Gubate.

Ya ce harin ya yi sanadiyar mutuwar wani magidanci direban tarakta, Mohammed Kabiru mai shekaru 35 da kuma raunata wani Hassan Lawan.

Kakakin ƴan sandan ya tabbatar da kama Magajin Garin bisa zargin hannu a wannan aika-aika, inda ya ce rundunar ƴan sanda na kan bincike, Daily Post ta kawo.

An kama ƴan fashi a Yobe

Ya ci gaba da cewa, a irin wannan yanayi, ‘yan sanda a Damagum sun kama wani Abduwahab Abubakar (40) da wasu mutum hudu da ake zargi da kai harin fashi.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama shugaban 'yan banga dauke da sassan jikin ɗan Adam

Mai magana da yawun ƴan sandan ya ce waɗanda ake zargin sun farmaki wani mai suna Hussaini Lawan Sani a kauyen Goba Abba inda suka masa fashin N250,000.

Matatar Ɗangote zata fara fitar da fetur

A wani rahoton na daban Mataimakin shugaban rukunin masana'antun Ɗangote, Devakumar Edwin ya ce man fetur zai shiga kasuwa a Yuli kamar yadda aka yi alƙawari.

Edwin ya ce matatar Dangote za ta samar da isasshen man fetur, kalanzir, dizal da man jirgi a Najeriya har ma a a fitar da su zuwa ƙasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262