Shekarar Hijira: Jerin Watanni 4 Masu Alfarma a Addinin Musulunci

Shekarar Hijira: Jerin Watanni 4 Masu Alfarma a Addinin Musulunci

  • A jiya Lahadi aka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 tun bayan hijirar Annabi mai tsira da aminci daga garin Makka
  • Addinin Musulunci ya ware watanni hudu na musamman masu alfarma a cikin watanni 12 da kalandar Musulunci ta kunsa
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku jerin watanni hudun da ayyukan falala da alheri daban daban da kowannensu ya kunsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A jiya al'ummar Musulmi suka shiga watan Muharram na shekarar 1446 wanda lissafin watannin shekarar Musulunci ya fara da shi.

A cikin watannin musulunci guda 12 akwai guda hudu da Allah mai girma da ɗaukaka ya zaba a kan sauran.

Kara karanta wannan

1446: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata Musulmi Ya Sani Dangane da Shekarar Hijira

Kalandar Musulunci
Watannin Musulunci masu alfarma. Hoto: Idara Furqan
Asali: UGC

A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku jerengiyar watanni hudu masu alfarma tare da falala da suka kunsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Watannin Musulunci masu alfarma a shekara

1. Watan Muharram

Watan Muharram shi ne na farko a cikin jerengiyar watanni 12 a kalandar Musulunci kuma yana cikin watanni masu alfarma.

Ana son yawaita ibadar azumi a cikin watan Muharram kamar yadda sunnar Annabi Muhammad (SAW) ta tabbatar.

Sheikh Muhammad Saleh ya wallafa a shafinsa cewa a ranar 10 ga watan Muharram ne ake azumi Ashura.

2. Watan Rajab

Watan Rajab shi ne na bakwai kuma yana cikin watanni masu alfarma kamar yadda Sheikh Muhammad Saleh ya wallafa a shafinsa.

Malaman Musulunci suna ganin cewa watan Rajab na cikin watanni da ya kamata Musulmi ya fara shiri domin tunkarar Ramadan.

3. Watan Zul Qadah

Kara karanta wannan

Malamai da limamai a Arewa sun yiwa masu son warware rawanin Sarkin Musulmi wankin babban bargo

Watan Zul Qadah shi ne wata na 11 a cikin jerengiyar watanni a kalandar Musulunci kuma yana cikin watanni hudu masu alfarma.

Watan Zul Qadah na cikin watanni da ake fara shirye-shiryen gudanar da ayyukan Hajji da ake yi sau daya a shekara.

4. Watan Zul Hijja

Watan Zul Hijja shi ne na 12 a kalandar Musulunci kuma yana cikin watanni masu alfarma da ake aikin Hajji a cikinsa.

A watan Zul Hijja ake ibadar layya kuma ana son azumtar kwanaki 10 na farkosa wanda ranar Arafa ce ta tara a cikin kwanakin.

A cikin watanni masu alfarma an haramta yin yaki kuma aikata sabon Allah yana jawo zunubi sosai a cikinsu kamar yadda ake ruɓanya lada.

Hutun shekarar hijira a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ba da hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH.

Kara karanta wannan

An kama jagora a PDP, Atiku Abubakar ya zargi 'yan sanda da cin zarafin 'yan kasa

Gwamnatin ta ayyana yau Litinin, 8 ga watan Yulin 2024 a matsayin ranar da ma'aikata ba za su je wuraren aiki ba a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng