Auren Jinsi: Hisbah ta Magantu Kan Jami'inta da Ya Bayyana a Bidiyon 'Wise Initiative '

Auren Jinsi: Hisbah ta Magantu Kan Jami'inta da Ya Bayyana a Bidiyon 'Wise Initiative '

  • Hukumar Hisbah ta binciko jami'inta da aka gani a bidiyon kungiyar nan mai rajin cusa ra'ayin auren jinsi a Kano
  • Shugaban hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce ba da yawun hisba jami'in ya je taron kungiyar a shekarun baya ba
  • Shi ma jami'in a jawabinsa, ya bayyana cewa an gayyace shi taron ne da sunan kare hakkin dan Adam amma bai san LGBTQ ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano- Hukumar Hisbah ta nesanta kanta da gayyatar kungiyar 'WISE' da aka gano ta na cusa ra'ayin auren jinsi da dangoginsa a Kano. Shugaban hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya yi jawabi bayan an gano jami'inta, Idris Ahmed Gama cikin bidiyon kungiyar.

Kara karanta wannan

"Ban san meye LGBTQ ba": Jami'in Hisbah ya magantu bayan kama shi da tallata auren jinsi

Daurawa
Hukumar Hisbah ta gano da ya fito a bidiyon kungiyar yada auren jinsi a Kano Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim daurawa
Asali: Facebook

A bidiyon da shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ba da yawunsu jami'in ya halarci taron ba.

Wise: Za a hukunta jami'in Hisbah

Hukumar Hisbah ta bayyana cewa za ta hukunta jami'inta da ya yi amfani da sunanta a taron kungiyar WISE da ke yada akidar auren jinsi. Shugaban hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayar da tabbacin, inda ya ce lokacin da jami'in ya halarci taron, hukumar ba ta san an yi ba. Ya kara da cewa babban laifi ne jami'i ta je taro da sunanta ba tare da sanin mahukuntan Hisbah ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Rufe mani abin aka yi," Jami'in Hisba

Jami'in hukumar Hisbah da aka gani a bidiyon kungiyar yada akidar auren jinsi da dangoginsa, Idris Ahmed Gama ya ce bai san abin da LGBTQ ke nufi ba a lokacin.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: An bankado bidiyon jami'in Hisbah yana tallata 'yancin alakar jinsi

Ya shaidawa manema labarai cewa kungiyar ta gayyace shi taron ne a Sabon Gari shekarun baya, inda aka shaida masa cewa taro ne na kare hakkin dan Adam.

Ana binciken kungiyoyi a Kano

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta umarci hukumar Hisbah kan binciken kungiyoyi da ke shigowa Kano.

Wannan ya biyo gano wata kungiya da ke amfani kananan kungiyoyi wajen yada manufar auren jinsi ta hanyar bayar da tallafi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.