Matatar Ɗangote Za Ta Fara Sayar da Man Fetur a Najeriya da Wasu Ƙasashe
- Yayin da ƴan Najeriya ke fatan samun sauki, matatar man Ɗangote mai ƙarfin ta ce gangar ɗanyen mai 650,000 za ta fara sayar da man fetur
- Mataimakin shugaban rukunin masana'antun Ɗangote, Devakumar Edwin ya ce man fetur zai shiga kasuwa a Yuli kamar yadda aka yi alƙawari
- Edwin ya ce matatar Dangote za ta samar da isasshen man fetur, kalanzir, dizal da man jirgi a Najeriya har ma a a fitar da su zuwa ƙasashen waje
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Mataimakin shugaban masana'antun Ɗangote (DIL) na sashen mai da gas, Devakumar Edwin ya tabbatar da cewa matatar Ɗangote za ta fara sayar da fetur a watan Yuli.
Edwin ya bayyana hakan ne yayin da ya fita rangadin duba yadda aiki ke tafiya matatar man da ke Ibeju-Lekki a jihar Legas.
Ya jaddada cewa kamar yadda aka yi alkawari tun farko, mai daga matatar Ɗangote zai fara shiga kasuwa cikin watan Yuli, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhimmancin matatar man Dangote
A cewarsa, hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen wahalhalun fetur a nahiyar Afirka da kuma tace ɗanyen man da ake haƙowa a cikin gida.
Mista Edwin ya ce kamfanin yana da burin samar da ingantaccen tsarin ci gaban masana'antu, samar da ayyukan yi da wadatar tattalin arziki.
Ya ce duk kayan da matatar take fitar wa suna da inganci kuma sun cika dukan sharuɗɗa da ƙa'idojin aiki na ƙasa da ƙasa, rahoton Leadership.
Najeriya za ta fita daga matsalar fetur
Ya ƙara da cewa matatar attajirin za ta samar da kashi 100% na man fetur, dizal, kalanzir da man jiragen sama da ake buƙata a Najeriya har a fitar da su ƙasashen waje.
Haka zalika kamfanin S&P Global ya ayyana matatar man Ɗangote a matsayin wada za ta warware ƙalubalen da suka mamaye hada hadar musayar kuɗi.
Ɗangote ya yi magana kan tattalin arziki
A wani rahoton kuma, an ji shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar nan zai farfado nan da watanni.
Ya bayyana haka ne jim kadan bayan shugaban kasa, Bola Tinubu ya rantsar da shi da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren kasuwanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng