"Kar Ku Ji Tsoron Komai", Masu Shigo da Fetur Sun Fadi Dalilin Karancin Mai
- Kungiyar masu kasuwancin makamashin man fetur (MEMAN) ta bayyana dalilan da ya sa aka samu karancin mai
- Kungiyar na bayanin ne bayan an samu karancin mai da ganin dogayen layi a wasu sassan Abuja da kuma Legas
- Babban sakataren kungiyar, Clement Isong ya bayyana cewa mamakin ruwa sama da tsawa ya sa aka dakata da dakon man
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja - Kungiyar 'yan kasuwa ta makamashin man fetur ta kasa (MEMAN) ta bayyana dalilin da ya sa aka samu karancin shigo da mai a kwanakin nan. Bayanin na zuwa ne bayan an samu bullar dogayen layuka a gidajen mai da ke Abuja da Legas da wasu sassan Kano a yan kwanakin nan.
Daily Trust ta wallafa cewa babban sakataren kungiyar, Clement Isong ya ce mamakon ruwan da ake yi ne ya kawo cikas wajen shigo da fetur gidajen mai.
MEMAN ta fadi dalilin karancin fetur
Babban sakataren yan kasuwar, Clement Isong ya ce mamakon ruwa da tsawo da ake samu kwanan nan ne ya kawo cikas wajen safarar fetur daga jirgi zuwa wani jirgin. Ya ce yanayin ya kuma taka rawa wajen dakatar da sauke fetur zuwa gidajen mai da ma safarar sa zuwa wuraren da ake bukata. Leadership News ta tattara cewa hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET) ta gargade su kan sauke fetur a wannan yanayi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Da hatsari sauke fetur a damuna," MEMAN
Clement Isong ya shawarci yan Najeriya da kar su ji tsoron komai ko sayen fetur domin su biye, saboda ba wata gagarumar matsala ba ce.
Ya kara da cewa man fetur da dangoginsa na saurin kamawa da wuta, saboda haka ne sai an yi taka tsan-tsan wajen sauke shi da safarar sa a wannan yanayin.
Shugaban ya kara da cewa matukar aka bijirewa gargadin NIMET, za a fuskanci matsala har da yiwuwar asarar rayuka.
An samu dogayen layin man fetur a Abuja
A wani labarin kun ji cewa an samu bullar dogayen ƙauyukan fetur a gidajen mai da ke babban birnin tarayya Abuja da Legas.
Wannan na zuwa ne bayan tarin bashi da kamfanonin da ke ba Najeriya mai ke bin kamfanin NNPCL bashin Dala Biliyan 6.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng