'Yan Bindiga Sun Bi Dare Sun Sace 'Yan Jarida 2 Tare da Iyalansu a Arewa

'Yan Bindiga Sun Bi Dare Sun Sace 'Yan Jarida 2 Tare da Iyalansu a Arewa

  • Ƴan bindiga sun kai sabon hari a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a ranar Asabar da daddare
  • Miyagun sun farmaki ƙauyen Danhonu a cikin Millennium City inda suka yi awon gaba da wasu ƴan jarida biyu tare da iyalansu
  • Ƴan bindigan dai sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 10:30 na dare sannan suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi kafin su sace mutanen

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan jarida biyu da iyalansu a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kai farmaki ƙauyen Danhonu da ke garin Millennium City inda suka shiga gidajen ƴan jaridar guda biyu sannan suka sace su tare da matansu da ƴaƴansu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan yiwa 'yan NYSC karin alawus

'Yan bindiga sun sace 'yan jarida a Kaduna
'Yan bindiga sun sace 'yan jarida biyu da iyalansu a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce ƴan jaridar sun haɗa da wakilin jaridar The Nation, Alhaji AbdulGafar Alabelewe da na jaridar Blueprint, AbdulRaheem Aodu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji AbdulGafar Alabelewe kuma shine shugaban ƙungiyar yan jaridu ta ƙasa (NUJ), reshen jihar Kaduna a halin yanzu.

Yadda ƴan bindiga suka sace ƴan jaridan

Wani ɗan uwan mutanen da abin ya shafa, Taofeeq Olayemi, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ƴan bindigan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Asabar, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Ya ce sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi kafin daga bisani suka yi awon gaba da mutanen.

Ya bayyana cewa sun sace Alhaji AlbdulGafar Alabelewe, matarsa da ƴaƴansa biyu yayin da suka sace Alhaji Aodu da matarsa sannan suka bar ɗiyarsa wacce ba ta da lafiya.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan tsige 'yan majalisa 25 da suka sauya bar PDP zuwa APC

"Da farko sun ɗauki Alhaji AbdulGafar, matarsa da ƴaƴansa uku da wata yarinya da take zama tare da su kafin daga bisani suka ce yarinyar ta dawo tare da ɗaya daga cikin yaran, inda suka tafi da AbdulGafar da matarsa da ƴaƴansa biyu."

- Taofeeq Olayemi

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ƴa bayyana cewa rundunar ƴan sandan na bakin ƙoƙarinta domin ganin an kuɓutar da mutanen.

"Eh lamarin ya auku muna bakin ƙoƙarinmu domin ganin mun kuɓutar da su."

- ASP Mansur Hassan

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan gudun hijira

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne ɗauke da makamai sun kashe mutane uku a jihar Benue.

Mutanen dai waɗanda ke rayuwa a sansanin ƴan gudun hijira na Agagbe sun rasa rayukansu ne lokacin da suke dawowa daga gonakinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng