An Sha Dakyar: Wutar Lantarki Ta Gyaru, an Ga Dawowar Wuta a Wasu Jihohin Najeriya

An Sha Dakyar: Wutar Lantarki Ta Gyaru, an Ga Dawowar Wuta a Wasu Jihohin Najeriya

  • Hankalin 'yan Najeriya ya kwanta yayin da wutar lantarki ta dawo a wasu jihohin kasar da daren yau
  • An fara shiga jimami da firgici bayan samun labarin lalacewar tushen wutar lantarki zuwa wani adadi mai muni
  • Wannan ne karo na hudu da Najeriya ke fuskantar kalubalen rashin wutar lantarki mai tsawo a cikin 2024

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Najeriya - Yayin da ake ci gaba da shirin shiga duhu sakamakon bacin wutar lantarki a Najeriya, yanzu haka wasu jihohi sun ga dawowar wuta a yankunansu.

Kamar a jihar Gombe, an dawo da wutar lantarki da misalin karfe 11:20 na dare, lamarin da ya jefa jama'a farin ciki da jin dadi.

Kara karanta wannan

Assha: Zaune bata kare ba a Najeriya, wutar lantarki ta sake baci a duk fadin kasa

A baya, rahoton da muka tattaro maku ya bayyana cewa, an samu tsaiko a tushen wutar lantarkin Najeriya, inda adadin wutar da ake samarwa ya sauka kasa sosai.

An dawo da wuta a Najeriya
An dawo da wuta a wasu jihohin Najeriya
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu jihohin kasar dai tuni sun yi sa'o'i babu wutar lantarkin, inda ake tunanin hakan zai shafi harkokin yau da kullum.

Yadda wuta take a jihar Kaduna

Wani mazaunin Kaduna, Aliyu Usman ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa, yankuna da dama suna da wutar lantarki har zuwa kusan karfe 10 na dare a ranar Asabar da ya tattauna da wakilinmu.

Da yake bayani, ya ce:

"Mun ga sanarwa a jaridu cewa wuta ta lalace, amma tun lokacin muna da wuta, watakila an shawo kan matsalar da wuri ne.
"A gaskiya na zaci za mu shiga damuwa kamar yadda a baya muka shiga matsalar wuta, amma Alhamdulillahi tun da bata kai ga haka ba.

Kara karanta wannan

Kano: Fusatattun matasa sun fatattaki wakilin Sanusi II daga Karaye bayan cire masu Sarki

"Rashin wutar nan na bata mana kasuwanci, amma ya muka iya, shugabanninmu da 'yan kasuwanmu basu da tausayi."

Lalacewar wuta a karo na hudu a 2024

Kun ji cewa, an sake samun rushewar tushen karafan rarraba wutar lantarki na Najeriya, inda yanzu kasar ke samar da 0.80MW na wutar lantarki.

Binciken da aka yi ya nuna cewa, wutar ta fara raguwa ne da kimanin karfe 2 na rana zuwa 2,797.16MW daga akalla 3,417.99MW da misalign karfe 1 na rana.

Wutar ta kara raguwa zuwa 1,020.08MW da misalin karfe 3 na rana kafin ta karasa raguwa sosai zuwa 0.80MW da misalin karfe 4 na yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.