Darajar Naira Ta Farfado Bayan Kwashe Kwanaki Tana Faduwa Kasa Warwas
- Bayan kwashe kwanaki uku darajar Naira tana faɗuwa a kasuwar canji, darajar kuɗin na Najeriya ta farfaɗo a ranar Juma'a
- A ranar juma'a, 5 ga watan Yulin 2024, darajar Naira ta kai N1,525 maimakon N1,535 da aka yi cinikinta a ranar 4 a watan Yuli
- Daga ranakun 2 zuwa 4 ga watan Yulin 2024, daraja Naira ta riƙa faɗuwa a kasuwar ƴan canji da kasuwar gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Darajar Naira ta farfaɗo bayan ta jera kwanaki uku tana faɗuwa a kasuwar ƴan canji a ranar Juma'a.
Naira ta ƙaru da kaso 0.98% zuwa N1,525/$1 a ranar, 5 ga watan Yuli daga N1,535/$1 da aka yi cinikinta a ranar 4 ga watan Yuli.
Naira ta farfaɗo a kasuwa
Ƴan kasuwar canji waɗanda aka fi sani da BDCs suna siyan kowace Dala a kan farashin N1,500 yayin da suke siyarwa a kan farashin N1,525, inda suka sanya ribar N25, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kasuwar gwamnati, darajar Naira ta farfaɗo bayan ta kwashe kwanaki uku tana faɗuwa ƙasa warwas.
A cewar bayanai daga kasuwar hada-hadar kuɗi ta FMDQ, an yi cinikin Naira kan farashin N1,509/$1 a ranar 5 ga watan Yuli, wanda hakan ya nuna an samu ƙarin kaso 0.7% daga farashin da aka siyar da ita na N1,520/$1 a ranar 4 ga watan Yuli.
Darajar Naira faɗi ƙasa
Daga ranakun 1 zuwa 4 ga watan Yulin 2024, darajar Naira ta faɗi a kasuwar ƴan canji da kasuwar gwamnati kafin ta farfaɗo a ranar 5 ga watan Yulin 2024.
A ranar 2 ga watan Yuli, darajar Naira a kasuwar ƴan canji ta karye zuwa N1,515/$1 daga farashin N1,510/$1 da aka yi cinikinta a ranar 1 ga watan Yuli.
Daga ranakun 3 zuwa 4 ga watan Yuli, darajar Naira ta ƙara faɗuwa zuwa N1,520 da N1,535, bi da bi.
A kasuwar gwamnati, darajar Naira ta faɗi zuwa N1,509, N1,512, da N1,520 daga ranakun 2 zuwa ga watan Yuli bi da bi.
CBN ya gargaɗi bankuna kan Naira
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya yi barazanar ladabtar da bankunan ajiyar kuɗi da suka ki amincewa da karbar lalatattun takardun Naira daga abokan hulɗarsu.
Gargaɗin na CBN na zuwa ne bayan abokan hulɗar bankunan sun fara ƙorafi kan cewa bankunan za su karɓar lalatattun kuɗin.
Asali: Legit.ng