Alkali Ya Yi Barazanar Daure Hadimin Gwamna Abba Kan Shari'ar Ganduje
- Alkalin babbar kotun tarayya Simon Amobode ya yi barazanar cewa zai iya daure duk hadimin gwamnan Kano da ya fassara hukuncinsa ba dai-dai ba
- Wannan na zuwa ne bayan ya yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shigar gaban kotun ya ne neman a dakatar da bincikensa a Kano
- Mai Shari'a Simon Amobode ya ce duk da ya na sane da cewa gwamna na sanye da rigar kariya, amma zai iya daure hadimansa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Mamaki ya kama wadanda su ka halarci zaman babbar kotun tarayya bayan an ji alkali Simon Ambode ya yi ikirarin zai iya daure daraktan yada labaran gwamna Abba Kabir Yusuf.
Sanusi Bature Dawakin Tofa shi ne mai magana da yawun gwamna Abbba gida-gida, kuma rahotanni sun ce sai da mai shari'a ya yi tambaya a kan ko ya na cikin kotun.
The Guardian ta wallafa cewa Mai Shari'a Simon Ambode ya kuma tambayi 'yan jaridar da ke kotun su bayyana kansu, amma mutum biyu ne kawai su ka yi hakan saboda tsoron abin da ka-je-ya-zo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A ba Sanusi takardar hukuncin yau,' Alkali
Mai shari'a Simon Ambode ya nemi a tabbata a mikawa mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa takardar hukuncin da ya zartar kan karar da tsohon gwamna Ganduje ya shigar.
Abdullahi Umar Ganduje ya kai koke gaban kotun ya na neman a dakatar da bincikensa da gwamnatin Kano ke yi kan zargin almundahanar kudin jama'a.
Da ya waiwaya ya nemi Sanusi Bature Dawakin Tofa bai gan shi ba, mai shari'ar ya bayyana cewa ya san gwamna na sanye da rigar kariya, amma tsaf zai iya kulle mukarrabansa.
Alkalin ya ce zai iya daure su idan su ka fassara hukuncin da ya zartar ba dai-dai ba, inda ya nemi a tabbata Sanusi Bature ya samu takardar hukuncin a hannunsa.
Kotun ta yanke hukuncin cewa alkalan kotun babbar jihar biyu da ke shugabantar kwamitin binciken Ganduje su ajiye aiki ko a daina biyansu albashi da alawus.
Ganduje ya yi nasara a kotu
A baya mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi nasara a karar da ya shigar gaban babbar kotun tarayya kan tuhumarsa da gwamnatin Kano ke yi.
Mai shari'a Simon Ambode ya umarci alkalai biyu da gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya su jagorancin kwamitin binciken Ganduje su ajiye aiki nan da wasu awanni.
Asali: Legit.ng