Rikicin Sarakuna da Gwamnoni: Majalisa Za Ta Saka Masarautu a Kundin Mulkin Najeriya

Rikicin Sarakuna da Gwamnoni: Majalisa Za Ta Saka Masarautu a Kundin Mulkin Najeriya

  • Majalisar wakilan Najeriya ta bayyana kokarin da take yi na ganin ta sanya masarautun gargajiya a cikin kundin tsarin mulkin kasa
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ta samun rigingimun sarauta a wasu jihohin Najeriya wanda ke kai ga batun tsige sarakuna
  • Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya ce tuni aka kafa komai domin tabbatar da hakan, kuma hakan zai inganta tsaron kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Bayan rikicin sarauta da ya barke a jihar Kano, da kuma jijitar jitar tsige sarkin Musulmi, a yanzu dai majalisar tarayya ta fara shirin baiwa masarautu matsugunni a kundin mulki.

Ba iya kare masarautu daga saukalen gwamnoni ba, majalisar tarayyar tana son kare martabarsu domin bunkasa yaki da rashin tsaro a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta binciki kwangilar aikin Mambila, za a dauko aikin wutar tun daga 1999

Kakakin majalisar wakilai ya yi magana kan sanya sarakuna a cikin doka
Majalisar wakilai ta ce ta kafa kwamitin tsara shigar da masarautu a kundin mulkin kasa. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Majalisa za ta daga darajar sarakuna

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, Tajudeen Abbas, kakakin majalisar wakilai, ya ce tsaron kasar zai inganta idan ya zama sarakunan gargajiya na da kariyar dokar kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ko a shekarar da ta gabata, kudurin dokar sanya masarautun gargajiya a cikin kundin tsarin mulkin kasar bai samu karbuwa a majalisar ba.

Sai dai da yake jawabi a wajen bikin cika shekara guda da kafa majalisar wakilai ta 10, Hon. Abbas ya ce ta majalisar za ta yi gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.

Kakakin majalisar ya ce majalisar za ta ba sarautun gargajiya matsugunni a tsarin mulki bisa ga sahalewar dokar kasar, in ji rahoton Channels.

Majalisa ta kafa kwamiti kan masarautu

Kakakin majalisa Abbas ya ce ya kafa kwamitoci na musamman guda biyu a lokacin da ya hau kan karagar mulki, domin tsara yadda za a sanya masarautu a cikin kudin mulki.

Kara karanta wannan

Majalisa ta amince a kirkiro hukumar cigaban jihohin Arewa, za a jira Tinubu ya sa hannu

“Mun kuma yi imanin cewa tsaron kasarmu zai kara inganta idan aka baiwa masarautun gargajiya ayyukan da ya dace a dokance.
“Akwai kwamitin da muka kafa domin dmin tsara hanyar baiwa masarautun gargajiya hurumi a doka a cikin wannan gyara na kundin tsarin mulkin da ke tafe."

- Rt. Hon. Tajuddeen Abbas.

Ana gyaran dokar kananan hukumomin Sokoto

A wani labarin, mun ruwaito cewa kudurin sabunta dokar kananan hukumomin jihar Sokoto ya tsallake karatu na daya, wanda ke da nufin rage karfin ikon Sarkin Musulmi.

An ce sabuwar dokar za ta rage karfin ikon Mai alfarma Alhaji Sa'ad Abubakar III, wanda ya haɗa da cire ikon naɗa hakimai ko masu naɗin sarki ba tare da izinin gwamnatin jihar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel