CREDICORP: Tinubu Ya Naɗa Shugabannin Hukumar Ba da Bashi ga Yan Najeriya

CREDICORP: Tinubu Ya Naɗa Shugabannin Hukumar Ba da Bashi ga Yan Najeriya

  • Shugaba kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nada sababbin mukamai a hukumar CREDICORP a ranar Laraba, 3 ga watan Yuli
  • An kirkiro Hukumar CREDICORP ce domin duba yiwuwar ba yan Najeriya bashi saboda inganta sana'o'i da tattalin arziki
  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi bayani na musamman ga sababbin shugabannin da ya daurawa alhakin lura da hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT Abuja - Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nada sababbin mukamai a ranar Laraba.

Bola Tinubu ya nada shugabannin da za su cigaba da gudanar da hukumar CREDICORP domin ba yan Najeriya bashi.

Shugaba Tinubu
Tinubu na nada sababbin mukamai. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da mai taimakawa shugaban kasa a harkokin sadarwa, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Ali Nuhu ya bayyana yadda zai tallafawa matasa masu hidimar NYSC a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanda Tinubu ya ba mukami a CREDICORP

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Injiniya Uzoma Nwagba a matsayin babban daraktan da zai shugabanci CREDICORP.

Sauran wadanda suka samu mukamai a hukumar akwai Aisha Abdullahi, Olanika Kolawale, da Dakta Armstrong Ume Takang.

Ayyukan hukumar CREDICORP a Najeriya

Bincike ya nuna cewa an kirkiro CREDICORP ne domin saukakawa ma'aikata hanyar samun bashi daga gwamnati, rahoton Channels Television.

Ana sa ran cewa ta hanyar CREDICORP kashi 50% na ma'aikata za su samu karbar bashi daga gwamnati a shekarar 2030.

Sakon Tinubu ga shugabannin CREDICORP

Shugaba Bola Tinubu ya ce yana fatan sababbin shugabannin za su yi kokari wajen kawo canji da ake buƙata.

Saboda haka shugaban kasar ya yi kira garesu da su tabbatar sun yi aiki da gogewa da suke da ita wajen tabbatar da yan Najeriya sun samu biyar bukata ta bangarensu.

Kara karanta wannan

"Muna tsoron faruwar irin zanga-zangar Kenya": Jigon APC ya gargadi Tinubu

Tinubu ya ba Farfesa Jega mukami

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba Farfesa Attahiru Jega babban mukami a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto.

Farfesa Attahiru Jega na cikin mutane 555 da shugaban kasar ya naɗa shugabancin kwamitocin gudanarwa a manyan makarantu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel