Hukumar NDLEA ta Kawo Batun Yin Gwajin Shan Kwaya Kan Masu Niyyar Aure
- Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta bayar da shawara kan yadda za a rage rabuwar aure a jihar Kano
- Shugaban hukumar a Kano, Abubakar Idris Ahmad ya bayar da shawarar a rika tilasta gwajin kwaya gabanin aure domin kakkabe al'adar
- Shugaban ya kara da cewa an gano cewa ana samun karuwar rabuwar aure a Kano, lamarin da ya ke ganin yin gwajin zai yake shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayar da shawara ga ma'aurata domin kare ta'ammali da miyagun kwayoyi tsakanin ma'aurata.
Shugaban NDLEA a Kano, Abubakar Idris Ahmad ya bayar da shawarar cewa a rika tabbatar da yin gwajin duba amfani da kwayoyi gabanin aure.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Abubakar Idirs Ahmed na ganin tilasta gwajin ta'ammali da kwayoyi kafin aure zai taimaka wajen kakkabe dabi'ar hana shan kwayoyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Gwajin kwaya zai rage ta'ammali da su," NDLEA
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa gudanar da gwaji kafin aure zai taimaka wajen gano matsalolin amfani da kwayoyi da wuri tsakanin ma'aikata.
Shugaban NDLEA a Kano, Abubakar Idris Ahmad ya ce za a iya samar da hanyoyin magance matsalolin shan kwaya idan an gano matsalar.
Ya ce akwai bukatar bayar da shawarar ganin yadda ake samun karuwar rabuwar auare da rage ta'ammali da miyagun kwayoyi a Kano, kamar yadda Pulse Nigeria ta wallafa.
Shugaban ya ce an gano idan akwai wanda ke shan kwaya a cikin ma'aurata, ya koyawa dan uwansa da yara wanda haka ke kara kabbama matsalar.
NDLEA ta kama dilolin kwaya 1000
A baya mun kawo labarin cewa hukumar yaki da sha da ta'ammali da miyagun kwayoyi ta kama masu safarar miyagun kwayoyi sama da 1,344 cikin shekara guda a Katsina.
Shugaban hukumar a jihar, Hassan Abubakar ne ya bayyana haka a cikin nasarorin da suka samu na yakar harka da miyagun kwayoyi a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng