Kungiyar Kwadago Ta Bayyana Matsayarta Bayan Sabon Karin Kudin Wutar Lantarki

Kungiyar Kwadago Ta Bayyana Matsayarta Bayan Sabon Karin Kudin Wutar Lantarki

  • Kungiyoyin kwadagon NUC da TUC sun nuna damuwa bayan kamfanoni masu rarraba wuta sun kara kudin lantarki a Najeriya
  • Yan kwadago sun ce abin Allah wadai ne a samu sabon karin kudin wuta bayan ba a gama tattaunawa a kan karin da aka yi a baya ba
  • Kamfanonin raba wuta sun bayyana dalilin karin kudin lantarkin duk da matsin rayuwa da ake fama da ita a Najeriya a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyoyin kwadago sun nuna rashin jin dadi kan yadda kamfanoni suka kara kudin lantarki a Najeriya.

A jiya Laraba ne kungiyar kwadago ta yi magana kan karin kudin da aka yiwa wadanda suke layin Band A.

Kara karanta wannan

Jihar Adada: Muhimman abubuwa 5 game da shirin kirkirar sabuwar jiha a Kudu maso Gabas

Ministan makamashi
Yan kwadago sun bukaci a rage kudin lantarki. Hoto: Hoto: Adebayo Adelabu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kamfanoni masu rarraba wutar lantarki sun yi bayani kan dalilin karin da aka samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudin wuta: Yan kwadago sun yi martani

Kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun yi Allah wadai da karin kuɗin lantarki da kamfanonin rarraba wuta suka kawo a cikin makon nan.

Yan kwadago sun ce har yanzu suna kira ga gwamnatin tarayya kan rage kudin wuta kuma wannan karin bai kamata ba, rahoton New Telegraph.

Kamfanonin da suka kara kudin wuta

A ranar Litinin da ta wuce ne kamfanonin rarraba wuta suka kara kudin lantarki ga yan layin Band A daga N206.80 zuwa N209.50.

Kamfanonin da suka kara kudin sun hada da kamfanin raba wuta na Ibadan, Kaduna, Legas da sauransu.

Dalilin karin kudin wuta a Najeriya

Kamfanonin sun ambaci tashin dala, karuwar farashin kayayyaki da gas cikin dalilan da suka janyo karin kudin.

Kara karanta wannan

An kwace kwangilar hanyar da ta haɗa Arewa da kudu a hannun Dantata da wasu kamfanoni

Duk da karin kudin, kamfanonin sun bayyana cewa za a cigaba da samun wutar lantarki yadda ya kamata a garuruwan Najeriya.

Karin kudin wuta: Minista ya magantu

A wani rahoton, kun ji cewa ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya caccaki masu sukar gwamantin tarayya kan karin kudin lantarki ga 'yan sahun Band A.

Ministan ya ce maganar cewa karin kudin wutar ya jawo tashin kudin kayan masarufi magana ce da ba za ta kama hankali ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng