Yadda Yan Sanda Suka Sasanta Sarki da Limami Bayan Rikici Kan Zuwa Aikin Hajji
- Kwamishinan 'yan sanda a jihar Oyo ya dauki matakin sasanta rikicin da ya barke tsakanin limami da babban basaraken Ogbomosho
- A makon da ya wuce ne mai sarautar Ogbomoso, Oba Ghandi Afolabi Olaoye ya kalubalanci limamin bisa zuwa Hajji ba tare da izini ba
- A jiya Laraba ne kwamishinan yan sandan ya sasanta Oba Ghandi Afolabi Olaoye da limami Yunus Tella Olushina Ayilara a ofis dinsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Biyo bayan saɓanin da aka samu tsakanin basarake da limami a jihar Oyo, kwamishinan yan sanda ya shiga lamarin.
An samu sabani ne tsakanin Oba Ghandi Afolabi Olaoye na masarautar Ogbomoso da limamin garin, Yunus Tella Olushina Ayilara a kan zuwa aikin Hajji.
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa a jiya Laraba ne kwamishinan yan sanda ya gayyacesu domin yin sulhu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin shigar yan sanda rikicin
An gano cewa kwamishinan ya shiga tsakanin limami da basaraken ne domin kaucewa fitinar da saɓanin zai iya haifarwa.
Rahotanni sun nuna cewa yan sanda sun dauki matakin ne domin kara tabbatar da doka da oda a cikin garin, rahoton Vanguard.
Abin da aka tattauna yayin sulhu
A lokacin sulhun, Oba Ghandi Afolabi da liman Yunus Tella sun bayyana abubuwan da suke kalubantar juna da su.
An tattauna abubuwan da suka hada da karya dokar aiki, yaɗa bayanai masu lahani a kafofin sadarwa, katsalandan da masarauta ke yi cikin limanci da tafiya aikin Hajji babu izini.
An yi sulhu tsakanin liman da basarake
A karshe kwamishinan yan sanda ya yi nasarar yin sulhu tsakanin liman Yunus Tella da Oba Ghandi Afolabi.
Sharudan sulhun sun hada da cewa liman zai ba Oba hakuri sai kuma janye karar da aka shigar a gaban kotu.
Kotu ta hana cire limami a Oyo
A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun jiha ta haramtawa basarake da 'yan majalisar masarautarsa daga tsige babban limamin Ogbomoso.
Rahotanni sun nuna cewa mai shari'a K.B. Olawoyin ya kwaɓi sarkin Ogbomoso, Oba Afolabi Ghandi daga tuɓe rawanin Sheikh Yunus.
Asali: Legit.ng