Babban Dan Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- An shiga jimami bayan rasuwar babban ɗan tsohon gwamnan jihar Oyo, Cif Kolapo Ishola a yau Laraba a jihar
- Marigayin mai suna Kunle Kolapo an tabbatar ya rasu ne da safiyar yau Laraba 3 ga watan Yulin 2027 a jihar
- Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin babban ɗan tsohon gwamnan ne da ya mulki jihar daga 19991 zuwa 1993
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da mutuwar babban ɗan tsohon gwamnan jihar Oyo, Kolapo Ishola.
Marigayin da ake kira Kunle Kolapo ya rasu da safiyar yau Laraba 3 ga watan Yunin 2024.
Oyo: Yaushe marigayin ya rasu?
Leadership ta tattaro cewa marigayin kafin rasuwarsa lauya ne kuma ya tsohon kwamishina a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kunle ya rike mukamin kwamishinan ne a mulkin tsohon gwamnan jihar, Otunba Christopher Alao-Akala.
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a bayyana musabbabin mutuwar babban ɗan tsohon gwamnan ba.
Har ila yau, iyalan basu fitar da wata sanarwa ba a hukumance kan babban rashin da suka tafka.
Mulkin tsohon gwamnan Oyo, Kolapo
Tsohon gwamnan ya mulki jihar Oyo ne daga shekarar 1991 zuwa 1993 a karkashin jam'iyyar SDP.
Ishola da aka haifa a watan Yunin 1934 ya jagoranci jihar ne a Jamhuriya ta uku wanda ya kawo ayyukan ci gaba musamman a bangaren ilimi.
Marigayin ya bar ofis ne a ranar 17 ga watan Nuwambar 1993 lokacin da marigayi Janar Sani Abacha ya hau mulki.
Daga bisani, Ishola ya rasu a ranar 9 ga watan Agustan shekarar 2011 yana da shekaru 77 a duniya.
Matashi ya hallaka mahaifinsa a Delta
A wani labarin, kun ji cewa wani matashi mai suna Ufuoma ya hallaka mahaifinsa wanda Fasto ne a jihar Delta.
Marigayin mai suna Issac Umurie ya rasa ransa ne yayin da yake tsaka da barci da tsakar daren yau Laraba 3 ga watan Yulin 2024.
Matashin har ila yau, ya farmaki mahaifiyarsa yayin da take kokarin kare mijinta da kuma dakatar da shi daga aikata hakan.
Asali: Legit.ng