Nnamdi Kanu: Obasanjo Ya Bayyana Abin da Ya Tattauna da Gwamnonin Kudu a Bayan Labule

Nnamdi Kanu: Obasanjo Ya Bayyana Abin da Ya Tattauna da Gwamnonin Kudu a Bayan Labule

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana bayan ya gana da gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya
  • A jiya Talata, 2 ga watan Yuli ne Olusegun Obasanjo tare da Cif Emeka Anyaoku suka gana da gwamnonin bayan sun aika musu gayyata
  • Mai taimakawa Obasanjo kan harkokin sadarwa, Kehinde Akinyemi ya bayyana abubuwan da Obasanjo ya tattauna da gwamnonin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Enugu - Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ƙaryata cewa ya gana da gwamnonin kudu maso gabas ne kan sake Nnamdi Kanu.

Olusegun Obasanjo ya ce gwamnonin sun gayyace shi ne domin tattaunawa kan wasu abubuwa na musamman.

Kara karanta wannan

Sanatocin kudu maso gabas sun gana da Ministan shari'a domin a saki Nnamdi Kanu

Obasanjo
Obasanjo ya fadi abin da ya tattauna da gwamnonin kudu maso yamma. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai taimakawa Obasanjo kan harkokin sadarwa, Kehinde Akinyemi ne ya yi karin haske kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Obasanjo ya tattauna da gwamnoni?

Kehinde Akinyemi ya ce tattaunawar Olusegun Obasanjo da gwamnonin ta fuskanci yadda za a inganta yankin kudu maso gabas ne.

Hadimin ya ce sai bayan sun gama tattaunawa da Obasanjo sannan gwamnonin suka yi magana kan neman sake Nnamdi Kanu.

Gwamnonin Kudu sun nemi saki Kanu

Bayan Obasanjo da Emeka Anyaoku sun gama tattaunawa gwamnonin yankin sai gwamnonin suka saka labule.

Kuma a karshen tattaunawar sun yanke cewa za su tunkari shugaba Bola Tinubu domin ganin an saki Nnamdi Kanu.

Cigaban da aka nema a yankin Kudu

Obasanjo ya ce gwamnonin sun gayyace shi tare da Cif Emeka Anyaoku domin tattaunawa kan matsalolin tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

An fasa kwai: Yadda aka raba cin hancin N250m domin Obasanjo ya shekara 12 a ofis

Ya kara da cewa sun kuma tattaunawa kan yadda za a haɓaka tattalin arziki yankin da samar da hadin kai, rahoton Vanguard.

Shehu Sani ya ceci Obasanjo a kurkuku

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda ya ceci Cif Olusegun Obasanjo daga hannun yan fursuna yayin da aka kullesu a gidan yari.

Shehu Sani ya bayyana cewa an kulle shi tare da Obasanjo a gidan yari a lokacin mulkin Janar Sani Abacha inda yan fursuna suka so lakaɗawa Obasanjo duka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel