Ali Nuhu Ya Bayyana Yadda Zai Tallafawa Matasa Masu Hidimar NYSC a Najeriya

Ali Nuhu Ya Bayyana Yadda Zai Tallafawa Matasa Masu Hidimar NYSC a Najeriya

  • Daraktan hukumar NFC, Ali Nuhu Muhammad ya gana da shugabar hukumar NYSC ta jihar Filato, Esther Ikupolalati
  • Ali Nuhu ya bayyana cewa zai tabbatar da walwalar masu yiwa ƙasa hidima da aka tura masana'antarsu ta shirya fim
  • Legit ta tattauna da wani mai hidimar kasa a karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa domin jin yadda shirin zai tallafa musu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Daraktan hukumar NFC, Ali Nuhu Muhammad ya fara kokarin bayar da gudummawa ga matasa masu hidimar NYSC.

Ali Nuhu ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da ya yi da shugabar hukumar NYSC ta jihar Filato, Esther Ikupolalati.

Kara karanta wannan

Yadda tirela ta wuntsila a Kano, mutane kusan 30 sun mutu

Ali Nuhu
Ali Nuhu zai tallafi matasa masu NYSC. Hoto: Ali Nuhu Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan ne cikin wani sako da Ali Nuhu Muhammad ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Nuhu zai tallafi yan NYSC

Ali Nuhu ya ce zai tabbatar da cewa matasan da aka turo masana'antarsu sun samu wadatattun kayan aiki domin kwarewa.

Ya kara da cewa sun yi tanadi domin tabbatar da walwalar matasan da basu gudunmawar da ta kamata.

Za a koyawa 'yan NYSC sana'ar fim

Haka zalika Ali Nuhu ya ce sun tattauna kan yadda za a shigar da koyon wasan kwaikwayo cikin sana'o'in da NYSC ke koyawa matasa.

Ali Nuhu ya ce hakan zai buɗe kofa ga matasan wajen koyon sana'o'i daban-daban domin dogaro da kai.

Har ila yau ya ce shigo da harkar koyon fim cikin NYSC zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin Najeriya.

A karshe, Ali Nuhu ya ce yana da tabbas kan cewa haɗakar za ta haifar da ɗa mai ido wajen inganta NYSC da ba matasan gudunmawa.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi fatali da karar da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya shigar kan gwamnati

Legit ta tattauna dan NYSC

Wani mai hidimar kasa a karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa, Aminu Abubakar ya zantawa Legit cewa za su yi farinciki da shirin.

Aminu ya ce dama irin abin da ya kamata a koyawa matasan kenan domin samun abin dogaro da kai bayan kammala hidimar kasa.

Hadiza Gabon ta shawarci mata

A wani rahoton, kun ji cewa shahararriyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu gabon ta ja hankalin ƴan mata masu shirin shiga sana'ar fim.

Hadiza Gabon ta ce abin da yafi dacewa da yan mata shi ne yin aure ko komawa makaranta domin inganta rayuwarsu maimakon shiga sana'ar fim.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng