"'Yan Najeriya Sun Kashe N16tr Wajen Siyan Janaretoci da Fetur," Gwamnatin Tarayya

"'Yan Najeriya Sun Kashe N16tr Wajen Siyan Janaretoci da Fetur," Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana maƙudan kuɗaden da ƴan Najeriya suka kashe wajen siyan janaretoci da man fetur domin samun wutar lantarki
  • Ministan makamashi, Bayo Adelabu, ya bayyana cewa a shekarar 2023 ƴan Najeriya sun kashe N16tr kan janaretoci da fetur
  • Ya bayyana cewa da za a sanya wani kaso na kuɗaden da ake kashewa kan janaretoci da fetur a ɓangaren makamashi, da za a daina ɗauke wuta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a shekarar 2023 kaɗai ƴan Najeriya sun kashe N16.5tr wajen siyan man dizal, man fetur da janaretoci domin samun wutar lantarki.

Gwamnatin ta sanar da cewa ɓangaren samar da wutar lantarki da ya haɗa da kamfanonin samar da wutan da rarraba ta, ya samu N1tr a matsayin kuɗaɗen shiga a shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi dalilin yin doka domin rage ikon Sarkin Musulmi

'Yan Najeriya sun kashe N16tr kan janaretoci da fetur a 2023
Ministan makamashi ya ce 'yan Najeriya sun kashe N16tr kan janaretoci da fetur a 2023 Hoto: @BayoAdelabu
Asali: Facebook

Ministan makamashi, Bayo Adelabu ya bayyana hakan a wajen taro mai da gas na Najeriya na shekarar 2024 a Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Najeriya sun kashe N16tr a 2023

Ya bayyana cewa da za a sanya wani kaso na kuɗaɗen da ake kashewa wajen janaretoci da man dizal domin samun wutar lantarki a ɓangaren makamashi na ƙasar nan, da ba a riƙa ɗauke wuta ba, rahoton da Within Nigeria ya tabbatar.

"Kuɗaden da ake kashewa a ɓangaren sun kusa N20tr. Sannan bari na faɗi wani abu, duka kuɗaɗen shigar da aka samu a ɓangaren samar da makamashi bai wuce N1tr a 2023 ba."
"Amma kuɗaɗen da aka kashe wajen siyan janaretoci, man dizal da man fetur ya kusa N20tr."
"Idan da za a sanya ko da kaso ɗaya bisa huɗu na kuɗaden a ɓangaren samar da makamashi, hakan zai sanya a ƙara samun kuɗaɗen shiga N5tr inda ɓangaren zai samu N6tr, tabbas za mu riƙa samun wutar da kusan ba a ɗaukewa a Najeriya."

Kara karanta wannan

NYSC: Gwamna ya ba kowane 'dan bautar kasa kyautar N200,000, ya dauki matasa aiki

- Bayo Adelabu

An ƙara kuɗin wutar lantarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin rarraba lantarkin Kaduna (KAEDCO) ya sanar da ƙarin kudin wuta ga abokan hulɗarsa da ke kan tsarin 'band A' daga N206.80/kwh zuwa N209.5/kwh.

Wannan ƙarin kuɗin wutar lantarkin zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Yuli, 2024, amma an fitar da sanarwar ƙarin ne a ranar 3 ga watan Yuli, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel