Bola Tinubu Ya Naɗa Mace a Matsayin Shugabar Hukumar FGSHLB Ta Ƙasa

Bola Tinubu Ya Naɗa Mace a Matsayin Shugabar Hukumar FGSHLB Ta Ƙasa

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Hajiya Salamatu Ladi Ahmed a matsayin sabuwar babbar sakatariyar hukumar ba da lamuni FGSHLB
  • Shugaban ƙasar ya tabbatar da wannan naɗi ne ta hannun shugabar ma'aikatan tarayya, Dokta Folasade Yemi-Esan ranar Talata a birnin Abuja
  • Hajiya Salamatu za ta maye gurbin Alhaji Ibrahim Mairiga wanda ya fara hutun gama aiki gabannin ƙarewar wa'adinsa a cikin watan Satumban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Hajiya Salamatu Ladi Ahmed a matsayin shugabar hukumar ba da lamunin gidaje (FGSHLB).

Shugabar hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dokta Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana hakan ranar Talata, 2 ga watan Yuli, 2024 a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan jami'in hukumar EFCC ya salwantar da ransa

Shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Bola Ahmed Tinubu ya nada sabuwar shugabar hukumar ba da lamunin gidaje Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Yemi-Esan ta sanar da wannan naɗi da shugaban ƙasa ya yi ne a lokacin da take miƙa takardar kama aiki ga Hajiya Salamatu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin wannan lokaci dai Hajiya Salamatu ta kasance daraktan sashen ayyuka a hukumar bayar da lamunin gidaje ta tarayya.

Tinubu ya nace mace a hukumar FGSHLB

Rahoton The Cable ya nuna cewa za a maye gurbin Alhaji Ibrahim Mairiga wanda ya fara hutun kammala aiki gabanin ƙarewar wa'adin shekaru huɗu a watan Satumba, 2024.

Yayin da take taya sabuwar shugabar hukumar FGSHLB murnar samun wannan matsayi, Misis Yemi-Esan ta buƙaci Hajiya Salamatu ta yi amfanin kwarewar aikin da take da shi wajen bunƙasa hukumar.

Shugabar ma'aikatan tarayya ta kuma roƙi wadda aka naɗa ta sa basira da gogewar da ta samu tsawon shekaru wajen tabbatar da an cimma manufar FGSHLB.

Kara karanta wannan

Fadar Sarkin Musulmi ta bayyana gaskiya kan rigima da gwamnatin Sokoto

Majalisa ta kinkimo kudirin ƙara jiha 1

A wani rahoton na daban a karo na biyu bayan rantsar da majalisar wakila, an gabatar da kudirin kirkiro ƙarin jiha ɗaya a shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya.

A wannan karon, ƴan majalisa biyar ne suka gabatar da kudirin neman kirkiro jihar Etiti kuma har an masa karatu na farko a zaman ranar Talata, 2 ga watan Yuni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel