An Gabatar da Kudirin Kirkiro Ƙarin Jiha 1 a Majalisar Wakilai, Ya Tsallake Karatu Na Farko

An Gabatar da Kudirin Kirkiro Ƙarin Jiha 1 a Majalisar Wakilai, Ya Tsallake Karatu Na Farko

  • Majalisar wakilan tarayya ta fara karatu na ɗaya kan sabon kudirin da ya nemi a kirkiro ƙarin jiha ɗaya a shiyyar Kudu maso Gabas
  • 'Yan majalisar wakilai biyar daga jihohin Abia, Imo, Enugu, Anambra da Ebonyi ne suka gabatar da kudirin kafa jiha mai suna Etiti
  • Kudirin ya bukaci a saka jihar Ekiti a cikin jerin jihohin Najeriya da ke kunshe a kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - A karo na biyu bayan rantsar da majalisar wakilai ta 10, an gabatar da kudirin kirkiro ƙarin jiha ɗaya a shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya.

A wannan karon, ƴan majalisa biyar ne suka gabatar da kudirin neman kirkiro jihar Ekiti kuma har an masa karatu na farko a zaman ranar Talata, 2 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi a shirye yake, zai karɓi kowacce dokar gwamnatin Sokoto

Majalisar wakilan tarayya.
An sake gabatar da kudurin kafa sabuwar jiha a Kudu maso Gabashin Najeriya Hoto: @NGRHouse
Asali: Facebook

Ana neman karin jihar Etiti a Najeriya

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, kudirin ya buƙaci a fitar da sabuwar jihar daga jihohi biyar na Kudu maso Gabas, Abia, Enugu, Anambra, Ebonyi da Imo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan majalisar da suka gabatar da kudirin sun haɗa da Amobi Ogah (LP, Abia), Miriam Onuoha (APC, Imo), Kama Nkemkama (LP, Ebonyi).

Sannan akwai Chinwe Nnabuife (YPP, Anambra) da Anayo Onwuegbu (LP, Enugu).

Jihar Etiti: Abin ɗa kudirin ya ƙunsa

A ɗan takaitaccen bayani kan kudirin ƙirƙiro jihar Etiti, an nemi sauya sassa uku na kundin tsarin mulkin ƙasar nan 1999.

Na farko, a goge kalmar 36 (jihohin Najeriya) a maye gurbinta da 37. Na biyu a saƙala sunan Etiti bayan Enugu a cikin jerin jihohin da ke cikin kundin tsarin mulki.

Abu na ƙarshe, kudirin ya buƙaci sauya jerin sunayen kananan hukumomi tare da zaro guda 11 daga jihohinsu na yanzu a mayar da su ƙarƙashin sabuwar jiha.

Kara karanta wannan

Hargitsi ya tashi a majalisar wakilai yayin da aka zargi mataimakin kakaki da nuna bambanci

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Isuikwuato da Umu-Nneochi (Abia), Orumba North da Orumba South (Anambra), Ivo da Ohaozara (Ebonyi), Aninri, Agwu da Oji River (Enugu), da Okigwe da Onuimo (Imo).

Yankin Kudu maso Gabas yana da mafi ƙarancin adadin jahohi daga cikin shiyyoyin ƙasar nan guda shida, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ina kudirin kirkiro jihar Orlu ya kwana?

Tun farko dai akwai wani kudurin da ya nemi kafa sabuwar jiha mai suna jihar Orlu a yankin Kudu maso Gabas, Ikenga Ugochinyere ya dauki nauyinsa.

Kudirin da Mista Ugochinyere ya gabatar ya raba kawunan ƴan majalisar Kudu maso gabas, inda wasu suka fito fili suna adawa da kirkiro jihar Orlu.

Majalisar Imo ta dakatar da mambobi 4

A wani rahoton kuma Shugaban majalisar dokokin jihar Imo, Hon Chike Olemgbe, a ranar Talata ya dakatar da ƴan majalisa huɗu bisa zargin shirin tsige shi.

Kara karanta wannan

NIN: Majalisar dattawa na kokarin kawo dokar da za ta shafi yan ƙasashen waje

Ya ce majalisar ta ɗauki wannan matakin ne a zaman sirri kuma daga yanzun an kwace dukkan kwamitocin da ke hannun ƴan majalisar da aka dakatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262