Gwamnatin Sokoto Ta Fadi Dalilin Yin Doka Domin Rage Ikon Sarkin Musulmi

Gwamnatin Sokoto Ta Fadi Dalilin Yin Doka Domin Rage Ikon Sarkin Musulmi

  • Daga ƙarshe gwamnatin Sokoto ta bayyana dalilin da ya sanya ta yiwa dokar ƙananan hukumomi da masarautun jihar garambawul
  • Kwamishinan shari'a na jihar ya bayyana cewa dokar da ake amfani da ita ta saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya
  • Ya yi bayanin cewa a idon doka Sarkin Musulmi bai da ikon yin naɗi domin hakan ya rataya ne a wuyan gwamna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta ce bisa kundin tsarin mulki, Sarkin Musulmi ba shi da ikon naɗa kowa.

Kwamishinan shari'a na jihar, Barista Nasiru Binji ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan dokar ƙananan hukumomi da masarautu ta Sokoto ta shekarar 2008.

Kara karanta wannan

NYSC: Gwamna ya ba kowane 'dan bautar kasa kyautar N200,000, ya dauki matasa aiki

Gwamnatin Sokoto ta fadi dalilin rage ikon Sarkin Musulmi
Gwamnatin Sokoto ta ce Sarkin Musulmi bai da ikon yin nadi Hoto: Sultan of Sokoto TV
Asali: Facebook

A wajen taron wanda aka yi a ranar Talata, kwamishinan ya bayyana cewa dokar da ake da ita a jihar ta saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta rage ikon Sarkin Musulmi?

Ya ce sashe na 76(2) na dokar ya saɓawa sashe na 5(2) na kundin tsarin mulkin 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

"Sashe na 5 (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya nuna cewa ikon yin naɗi a jiha yana ƙarƙashin gwamna ne ko ta hannun mataimakinsa, kwamishinoni ko wani wakilin gwamnati wanda gwamnan ya ba dama.
"Saboda haka babu wani ikon da aka ba majalisar Sarkin Musulmi ta yi naɗi. Sashe na 76(2) na dokar ƙananan hukumomin Sokoto da masarautu ya ba majalisar ikon naɗa Hakimai da Dagatai a jiha amma tare da amincewar gwamna mai ci."

Kara karanta wannan

Fadar Sarkin Musulmi ta bayyana gaskiya kan rigima da gwamnatin Sokoto

"Domin haka sashen bai dace da kundin tsarin mulkin shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima ba saboda haka ba zai yiwu a ci gaba da tafiya a haka ba."
"Saboda ikon yin naɗi yana ɓangaren zartaswa ne kuma wanene ya ke da wannan ikon, shin ba gwamna ba ne? Wannan shi ne dalilin da ya sa za a yi gyaran. Domin a gyara kuskuren da aka yi a baya."

- Barista Nasiru Binji

An gargaɗi gwamnatin Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa cibiyar ɗabbaƙa shari'ar Musulunci ta gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto kan wasa da rawanin Sarkin Musulmi.

Cibiyar ta tura gargaɗin ne yayin da ake zargin majalisar dokokin jihar ta tabbatar da wata doka da zata rage ikon Sarkin Musulmi kan naɗin Hakimai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng