NYSC: Gwamna Ya Ba Kowane Ɗan Bautar Kasa Kyautar N200,000, Ya Ɗauki Matasa Aiki
- Gwamna Umar Bago ya gwangwaje matasan da aka tura Neja aikin bautar ƙasa (NYSC) da abubuwan alheri a wurin rantsar da su
- Bago ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta ɗauki malaman lafiya daga cikinsu aiki, sannan za ta turawa kowane kyautar N200,000
- Bugu da ƙari gwamnan ya bayar da gudummuwar N5bn domin karasa ginin sansanin NYSC da ke ƙaramar hukumar Paikoro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ɗauki matasa masu yiwa ƙasa hidima aiki, waɗanda suka karanci likitanci da sauran fannonin kiwon lafiya.
Umaru Bago ya sanar da cewa gwamnatinsa ta ɗauke su aiki ne domin kawo ƙarshen mutuwar likitoci da sauran malaman lafiya a Asibitocin jihar Neja.
Masu NYSC a jihar Neja sun more
Gwamnan a bayyana haka ne a wurin rantsar da matasa 1,600 da aka tura jihar a rukunin B kashi na 1 na 2024 a sansanin NYSC da ke Paiko, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a wurin rantsar da ƴan bautar kasa, gwamnan ya ce:
"Muna da tsarin ɗaukar aiki kai tsaye ga matasa ƴan bautar ƙasa waɗanda suka karanci likitanci da sauran fannonin lafiya, saboda haka idan ka san fannin lafiya ka karanta, gwamnatin Neja ta ɗauke ka aiki."
Ya kuma sanar da bayar da gudunmuwar Naira biliyan biyar domin kammala aikin gina sansanin NYSC na dindindin a garin Paiko, hedkwatar ƙaramar hukumar Paikoro.
Gwamnan Neja ya ba matasan kyautar kuɗi
Har ila yau Gwamna Bago ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta bai wa dukkan matasa 1,600 da aka turo jihar domin su yiwa ƙasa hidima alawus ɗin N200,000.
A rahoton The Nation, Bago ya ƙara da cewa:
"Ina muku maraba zuwa jihar Neja, mu manoma ne, kamar yadda na saba faɗa a ko ina, ina mamakin yadda matashi zai gama jami'a ko kwalejin fasaha amma ya tsaya jiran aikin albashin N60,000.
"Mu a nan jihar Neja a abinci kaɗai ina kashe N500,000 duk wata. Duk wanda aka turo jihar Neja za mu ba shi kyautar N200,000 daga gonakin Neja. Na fahimci ku 1,600 ne, kowanen ku zai ji shigowar N200,000."
Matar mataimakin gwamnan Neja ta rasu
Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya karɓi rayuwar uwargidar mataimakin gwamnan jihar Niger, Hajiya Zainab Garba.
Gwamnan jihar Niger, Alhaji Mohammed Umaru Bago ne ya sanar da hakan a yau Talata a cikin sakon ta'aziyyar da ya fitar.
- Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng