NSCDC Ta Kama Ɗan Damfara da Ya Karbi N4.5m Domin Samar da Kujerun Hajji

NSCDC Ta Kama Ɗan Damfara da Ya Karbi N4.5m Domin Samar da Kujerun Hajji

  • Hukumar tsaro ta NSCDC ta reshen jihar Kwara ta baje kolin barayi da miyagu da ta kama da laifuffuka mabanbanta a faɗin jihar
  • Cikin miyagun da hukumar ta kama akwai dan damfara da aka zarga da karɓar makudan kudi domin yin hanyar zuwa aikin Hajji
  • Sauran miyagun da hukumar NSCDC ta kama sun hada da barayi masu shiga gidaje da aikata sauran laifuffuka daban-daban

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Hukumar tsaro ta NSCDC ta kama mutane da dama wadanda suka aikata laifuffuka daban-daban.

Ciki wadanda hukumar ta kama akwai wanda ake zargi da yin damfara domin yin hanyar tafiya aikin Hajji a Saudi.

Kara karanta wannan

Kano: KEDCO ya yanke wutar lantarkin jami'ar Dangote saboda taurin bashi

Hukumar NSCDC
Hukumar NSCDC ta kama miyagu a Kwara. Hoto: NSCDC KWARA STATE Command
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne cikin wani sako da hukumar NSCDC reshen jihar Kwara ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai damfara zuwa aikin Hajji

Hukumar NSCDC ta tabbatar da kama Ganiyu Yusuf Olalekan da ake zargi da karɓar kudi N4.5m a wajen Ibrahim Mustapha.

Ganiyu Yusuf Olalekan ya karbi kudin ne domin yiwa Ibrahim Mustapha hanyar samun kujerun Hajji guda uku.

Dama dai Ganiyu Yusuf ya karbi kudin ne da sunan cewa shi jami'in ma'aikatar kudi ta jihar Kwara ne, rahoton Daily Trust.

NSCDC ta kama barayi a Kwara

A daya bangaren, hukumar NSCDC ta tabbatar da kama Saliu Jimoh bisa zargin satar wayar wutar lantarki a gidan da ake kokarin kammalawa.

Haka zalika hukumar ta kama Mumini Kabir da satar bubur da wasu kayayyaki, sai kuma Ibrahim Wasi'u da aka kama da aikata laifi.

Kara karanta wannan

Kwara: Hukumar kwastam ta tatso harajin N10bn a cikin watanni 5

Hukumar ta tabbatar da cewa dukkan waɗanda aka kama sun amince da laifinsu kuma ana shirin kai su gaban alkali bayan kammala bincike.

An kama yan damfara a Makka

A wani rahoton, kun ji cewa biyo bayan matakan tsaurara tsaro da kasar Saudiyya ta dauka a kan aikin Hajji, ta kama yan damfara guda hudu.

Jami'an tsaron Saudiyya na musamman masu kula da ayyukan Hajji ne suka kama mutanen tare da bayyana dabarun da suke domin damfarar mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel