Sojojin Najeriya Sun Cafke Mata 3 Bisa Zargin Taimakawa Ƴan Bindiga a Kaduna

Sojojin Najeriya Sun Cafke Mata 3 Bisa Zargin Taimakawa Ƴan Bindiga a Kaduna

  • Sojoji sun kama wasu mata uku masu tallar zuma a bakin titin bisa zargin yiwa ƴan bindiga leƙen asiri a jihar Kaduna
  • Rahotanni sun nuna cewa an kama waɗanda ake zargin ne a kusa da kauyen Dogon Daji da ke ƙaramar hukumar Kagarko
  • Wannan na zuwa ne mako ɗaya bayan sojoji sun cafke wasu ƴan fashin daji a kasuwar kauyen SSC da ke kusa da Jere

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Sojoji sun damke wasu mata uku da ke talla a bakin titi bisa zargin bai wa ƴan bindiga bayanan sirri a ƙauyen Dogon-Daji da ke ƙaramar hukumar Kagarko a Kaduna.

Wani mazaunin garin, Yakubu Ishaku ya bayyana cewa asirin waɗanda ake zargin ya tonu ne a lokacin da dakarun sojojin Najeriya suka kai samame yankin.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane sun mutu yayin da ginin katafaren Otal ya rufta a Abuja

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya sun kama mata 3 masu tallatar zuma da zargin taimakawa ƴan bindiga a Kaduna Hoto: Nigeria Army
Asali: Twitter

Ya ce sojojin sun cafke matan da ake zargin a lokacin da suke sintiri a kewayen kauyen da kauyen da ke makwaftaka Kadara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda asirin matan ya tonu a Kaduna

Mutumin ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan sojoji sun samu bayanai daga bakin wasu ƴan leƙen asirin ƴan bindiga da aka kama makonni biyu da suka shige.

Wani shugaban al’ummar da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da kama mata guda uku da zargin yiwa ƴan bindiga leke asiri.

"Eh haka labarin yake, sojoji sun kama mata uku a kusa da Dogon-Daji makon jiya. Na yi mamakin yadda matan da ke tallar zuma a bakin titi za su iya zama imfoma."

Sojoji sun kama ƴan bindiga

Sahara Reporters ta tattaro cewa kwanan nan sojoji suka kama wasu ƴan fashin daji a kauyen SSC da ke kusa da garin Jere lokacin da suka kai samame kasuwar ƙauyen.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka sace basarake da wasu bayin Allah a Arewa

Bayanai sun nuna cewa kasuwar kauyen SSC na ɗaya daga cikin kasuwannin da aka ga baƙin ƴan kasuwa masu sayar da shanu, raguna, tumaki da wasu kayan abinci.

Har kawo yanzu jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai ce komai ba game da kama masu talla uku da ke taimakon ƴan bindiga ba.

An kashe ƴan sanda a Katsina

A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun yiwa ayarin jami'an tsaro kwantan ɓauna a yankin ƙaramar hukumar Jibia da ke jihar Katsina da safiyar ranar Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun kashe ƴan sanda huɗu nan take, sannan wani ɗaya ya rasu bayan an kai shi asibiti.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel